Kasashen Faransa, Australia da kuma tarayyar Turai sun jingine tattaunawar da suka fara game da zargin da Faransa ke yi wa Amurka na cin amanarta wajen karbe yarjejeniyar da ta kulla da Australian na samar mata da jiragen yakin karkashin teku.
A watan da ya gabata ne dai kasar Australia ta warware yarjejeniyar kasuwanci da ta kulla da kasar Faransa ta miliyoyin daloli don samar mata da jiragen yakin karkashin teku, kuma nan take ta maye yarjejeniyar da kasar Amurka.
Wannan al’amari dai a iya cewa ya taba kyakyawar dangantakar da ke tsakanin Amurka da Faransa, saboda yadda Faransan ta zargi Amurka da kulla kutungwilar da ta sanya Asutarilan ta sauya matsayar ta tun da fari.
Tuni dai Faransa ta fito karara ta shaidawa duniya cewa daga yanzu ba zata sake amincewa da gwamnatin Australia ba, tana mai ayyanata a matsayin wadda bata iya tsayawa kan magana daya, abinda ke zuwa bayan ta janye jakadun ta daga Australian da Amurka.
A cewar Faransan ko da dage tattaunawar na zuwa ne sakamakon yadda ministan kasuwancin Austarlian Dan Tehan ya gaza bayyana a gurin da aka shirya tattaunawar, bayan kuma yayi alkawarin yin hakan.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa tattaunawar ta biyo bayan gagarumar matsalar data kunno kai tsakanin kasar faransa da amurkan a sakamakon faransan da take zargin amurkan da cin amanar ta a kunshin yarjejeniyar sayar da makaman yakin ruwa ga australiya.
Kasashen yammacin turai dai sun mayar da hada hadar makamai wata babbar hanyar samar da kudin shiga wanda hakan ke kawo ci baya mai tsanani bangaren samar da tsaro gami da zaman lafiya a duniya baki daya, musamman a yankin asiya da afirka wadanda su aka fi saarwa da makaman da ake kerawa a turai din.