Kasar Amurka ta yi kira ga ‘yan takarar shugaban kasa a zabukan da aka yi a makon da ya wuce a kasar nan da su bi hanyar doka domin neman hakkinsu musamman a kan korare-korafen zaben.
Kakakin kasar Ned Price ne ya yi wannan kiran a cikin sanarwar da ya fitar a yau alhamis, inda sanarwar ta ce, akwai matakan shari’a da ya kamata ko wanne dan takara ya yi amfani da su don neman hakkinsa.
Sanarwar ta ce, mun fahimci ‘yan Nijeriya da dama da wasu jamiyyun ba su ji dadin yadda sakamakon zaben ya zo masu ba, sun kuma nuna damuwar su akan na’urar da aka gudanar da zaben da ita a karon farko a kasar.
A cewar sanarwar, muna kira ga magoya bayan ‘yan takarar da su guji furta kalaman da za su haifar da rikici a kasar.
Amurka ta kuma yi kira ga The US also (INEC) da ta lalubo da mafita akan matsalar da masu jefa kuri’a suka fuskanta da na’ura BVAS ta zabe kafin zuwan zabukan ranar 11 ga watan maris din 2023.
Amurka ta kuma ta ya sabon shugaban kasar da aka zaba Bola Tinubu murna kan lashe zaben.
(Abubakar Abba)
Source:Leadershiphausa