Amurka ta bukaci ‘yan kasar ta da su gaggauta ficewa daga sassan Habasha a dai dai lokacin da kungiyoyin ‘yan tawaye da dama suka sanar da kulla kawance da juna a wani yunkuri na hada karfi dpn afkawa birnin Adis Ababa da ke matsayin fadar gwamnatin kasar.
A kiran da Amurka ta yi da yammacin yau juma’a ta bukaci mutanenta da ke kowanne yanki na kasar su gaggauta ficewa don kaucewa rikicin da ka iya barkewa a kasar ta nahiyar Afrika matakin da ke zuwa bayan kawancen Oromo da ‘yan tawayen TPL na yankin Tigray wadanda ke da nufin hada karfi don afkawa dakarun gwamnati.
Tun a shekaranjiya laraba ne ‘yan tawayen suka kwace birnin Kemissie da ke lardin Amhara mai tazarar kilomita 325 a arewacin birnin na Adis Ababa, lamarin da ke kara sanya fargaba dangane da makomar kasar.
Tuni Firaminista Abiy Ahmed ya sanar da kafa dokar ta baci a fadin kasar, tare da yin kira ga Al’ummar kasar da su kasance cikin shirin kare kasar daga wadanda ya bayyana su a matsayin makiya.
A wani labarin na daban gwamnatin Habasha ta ce ‘yan tawayen kungiyar TPLF da ke yankin Tigray, sun kashe matasa akalla dari daya a farmakin da suka kai garin Kombolcha da ke arewacin kasar karshen makon da ya gabata.
Sanarwar gwamnati ta ce bai kamata kasashen duniya su kawar da kai a game da tu’annantin da ‘yan tawayen na Tigray ke aikatawa kan fararen hula a garuruwan da suka kwace daga hannun dakarun gwamnatin kasar ba.
Lokacin da kamfanin dillancin labaran Reuters ya nemi jin ta bakin kakakin ‘yan tawayen Getachew Reda dangane da wannan zargi da gwamnati ke yi masu, ya ki ya ce uffan dangane da hakan.
A cikin kwanaki biyu da suka gabata, ‘yan tawayen kungiyar ta TPLF sun kwace birane biyu daga hannun dakarun gwamnati, da suka hada da Kombolcha da kuma Dessie da ke arewacin kasar ta Habasha.