An bankado yadda manyan hafsosin Soji suka wawure kudin makaman da gwamnatin tarayya ta basu Hafsoshin Sojin mutum uku kadai sukayi almundahanar da babakere da kudi kimanin bilyan goma sha hudu lokacin suna sabis Daya daga cikinsu yayi kokarin fita kasar waje amma jami’an hukumar Immigration sun tsareshi, sun hanashi fita.
Gwamnatin tarayya ta hana tsohon shugaban hafsan Sojin kasa, Laftanan Janar Kenneth Miniman (mai ritaya) fita daga Najeriya bisa zargin hannu cikin satar kudin makamai N13.8bn.
Hukumar shiga da fice NIS ta bayyana hakan a martanin da ta mayar wa kotu bisa shigar da ita kara da Minimah yayi a Abuja, rahoton TheNation.
Yace jami’in ya ci mutuncin sa kuma yayi masa barazana don kawai ya fita kasar waje.
Amma a martanin hukumar NIS, Umar ya ce ya dakatad da Janar din ne bisa umurnin Gwamnatin tarayya ta ofishin hukumar hana almundahana da yaki da rashawa, EFCC.
Hukumar shiga da fice ta bayyanawa kotu cewa: “Ba’a yiwa mutumin barazana ko wulakanci ba a tashar jirgin Nnamdi Azikwe ba kamar yadda yake ikirari.”
“Bil hakki aka kwace fasfot din mutumin. Ba take hakkinsa na bil adama.” “EFCC sau biyu ta bukaci mu sanya masa ido.”
Alkali Inyang Ekwo ya dage zaman zuwa ranar 1 ga Maris. Rahoton binciken da akayi kansa Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta samu rahoto daga kwamitin binciken kudin makamai daga 2007 zuwa 2015, karkashin jagorancin tsohon Soja, Jon Ode.
Rahoton yace tsakanin 2010 da 2015 hukumar ta karbi makudan kudade amma wasu suka zuba kudaden aljihunsu.
Rahoton yace: “Biliyoyin Naira da hukumar Soji ta samu daga wajen Gwamnatin tarayya don sayen makami amma an gano wasu manyan Soji suka wawure kudin.”
“Mutanen da sukayi almundahanar Bilyan goma sha uku (N13,798,619,309) sune tsohon shugaban hafsan Soji, Laftanal Janar Kenneth Miniman; shugaban kasafin kudin hukumar Soji, Manjo Janar A. O Adetayo da tsohon diraktan kudi na hukumar, Birgediya Janar R. I Odi.”
Ya akayi da kudaden Rahoton ya cigaba da cewa: “An tura wadannan kudaden daga baitul malin Soji zuwa asusun bankunan kamfanonin wadannan mutane da basu da wata alaka ta kasuwanci da hukumar Soji.”
“Hukumar Soji da Gwamnatin tarayya sun yi asara matuka sakamakon riban da wadannan hafsoshin sukayi da kudaden nan don amfanin kansu.”
EFCC tace sakamakon wannan bincike, ta rubuta wasika ga hukumar Soji ta mika mata wadannan Sojoji uku don a gurfanar da su, kuma ya kamata ace an yi tun Satumban 2020.