Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya, Ahmed Attaf ya ce kasarsa da ke arewacin Afirka na tattaunawa da sojojin Nijar don ganin sun mika mulki ga farar hula cikin watanni shida.
Daily trust ta bayyana cewa, Kamfanin dillancin labaru na reuters ya bayar da rahoton cewa, Attaf, wanda a kwanakin baya ya zagaya kasashen yammacin Afirka, ya shaida cewa, “Mafi yawan kasashen da muka tattauna da su, na adawa da amfani da karfin soji wajen mayo da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar”.
A makon da ya gabata ne shugabannin sojojin kungiyar ECOWAS suka yi taro a Ghana domin tattaunawa kan yiwuwar daukar matakin soji a Nijar bayan da jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka hambarar da gwamnatin Bazoum suka mika mulki ga shugabannin sojoji a kasar.
Aljeriya a lokuta da dama, ta bayyana karara cewa tana adawa da matakin soji, sabida rashin zaman lafiya da ya biyo bayan shigar kungiyar NATO a Libya a shekarar 2011 inda aka hallaka tsohon shugaban kasar, Muammar Gaddafi.
Shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya bukaci a bashi dama ya mika wa gwamnatin farar hula mulki cikin shekaru uku a tattaunawar da ya yi da hukumomin Aljeriya tun bayan juyin mulkin, a cewar Attaf.
A makon da ya gabata ne gidan talabijin na kasar Aljeriya ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune ya ki amincewa da bukatar Faransa na tura sojoji domin yakar sojojin Nijar.
Sai dai Faransa ta musanta wannan rahoton.
Source: LEADERSHIPHAUSA