Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato zai saya wa kansa kasaitattun motocin alfama na Naira biliyan daya.
Majalisar zartaswar jiha ce ta aminta da saya wa gwamnan motocin kamar yadda Kwamishinan Matasa, Jamilu Gosta ya bayyana a sakamakon taron kashi na uku a fadar gwamnati a yau.
Ya ce “majalisar ta aminta da sayawa ofishin gwamna motocin hawa na alfarma na kimanin naira biliyan 1 da miliyan daya da dubu 250 an kuma yar da kwangilar ne ga kamfanin motoci na BT.”
A jawabinsa Kwamitin Yada Labarai, Sambo Bello Danchadi ya bayyana cewar gwamnatin jiha ta kashe naira miliyan 488 wajen kawata titin fadar gwamnati.
An kuma kebe naira biliyan 1 da miliyan 756 wajen sanya hasken wuta mai aiki da rana a hanyoyi 39 da ke cikin birmin jiha.
A nasa jawabin, Kwamishinan filaye da gidaje, Nasiru Aliyu Dantsoho ya bayyana cewar taron na majalisr zartaswar ya aminta da shimfida hanyoyin mota a Runjin Sambo kan naira biliyan 2, 189, 228. Ya ce sun kuma aminta da aikin sake shimfida titin Bodinga kusa da titin Maiduguri kan naira miliyan 816, 289.
A Labaran wasanni kuma dan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Alex Iwobi ya jefa kwallaye biyu a wasan da kungiyarsa ta Fulhma ta lallasa abokiyar karawarta Nottingham Forest da ci 5-0.
Iwobi ya fara jefa kwallo a minti na 30 da fara wasan kafin ya jefa ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Iwobi ya koma Fulham daga kungiyar kwallon kafa ta Everton a bana, inda zuwa yanzu ya jefa kwallaye 4 a wasanni 13 da ya buga mata.
Source: LEADERSHIPHAUSA