Akalla mutane 5 jami’an tsaro suka harbe har lahira a zanga zangar da aka gudanar yau a kasar Sudan domin adawa da juyin mulkin da sojoji suka sake gudanarwa a kasar bayan sun kawar da gwamnatin rikon kwarya.
Zanga zangar na zuwa ne kusan makwanni 3 bayan da Babban hafsan sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kawar da gwamnatin rikon kwarya da kuma tsare shugabannin fararen hular dake ciki, yayin da ya kafa dokar ta baci.
Kungiyar likitocin Sudan ta tabbatar da kashe masu zanga zanga guda 5 yau asabar a zanga zangar da aka gudanar a Khartoum da Omdurman da kuma wasu birane guda 3 dake gabashin Khartoum.
Majiyoyin asibiti sun ce 4 daga cikin wadanda suka mutu, sun rasu ne sakamakon harbin bindiga, yayin da guda kuma ya mutu sakamakon shakar iskar hayaki mai sa hawaye.
Rahotanni sun ce wasu mutane da dama sun samu raunuka sakamakon harbe harben da jami’an tsaro suka yi.
Wata majiya tace jami’an tsaro sun kutsa kai wani asibiti dake Omdurman inda suka tsare mutane da dama da suka samu raunuka.
Mutuwar mutanen akalla 5 ya kawo adadin mutanen da suka mutu zuwa 20 tun bayan fara zanga zangar adawa da juyin mulkin sojin da aka fara ranar 25 ga watan Oktobar da ta gabata.
Gidan talabijin din gwamnati ya sanar da cewar jami’an tsaro akalla 39 suka samu raunuka lokacin zanga zangar, kuma wasu raunukan sun yi tsanani.
Yan Sanda sun zargi masu zanga zangar da kai hari akan ofisoshin su, yayin da suka musanta amfani da harsasai akan masu adawa da juyin mulkin.