Jam’iyyar APC ta saki sabbin sunaye na mambobin kwamitin yakin neman zaben dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bayan ta yi yan gyare-gyare a wanda ta fitar a baya.
Har yanzu shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakalla na nan a matsayin mataimakin darakta a bangaren masu nishadantarwa na kwamitin kuma zai jagorancin yankin arewa maso yamma.
Jarumi Nuhu Abdullahi na nan a matsayinsa na mataimakin mai kula da jin dadin kwamitin yan wasan.
Sani Idris Moda ma yana nan a cikin kwamitin.
Sai dai kuma, a wannan karon, ba a ga sunan shahararren mawakin siyasa, Daudu Kahutu Rarara ba a cikin wanda a da shine ke rike da mukamin jami’in kula da harkokin kwamitin na yan wasa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Rarara ya saki sabuwar waka inda ya soki Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano.
A cikin sabuwar wakar da ya fitar don yi wa Tinubu kamfen, Rarara ya tabbatar da rikicinsa da Ganduje kuma ya bayyana gwamnan a matsayin ‘Hankaka’, ma’ana mutum mai fuska biyu.
Rarara kuma ya zargi Ganduje da daƙile saka sunansa a kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC.
A wani labarin, wata kungiyar goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai suna Jagaban National Coalition ta fara bi gida-gida tana yi masa kamfen.
Jagoran kungiyar a jihar Plateau, Mista Zakariyau Adigun, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a garin Jos, a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba.
Adigun ya ce shirin kungiyar shine sanar da duk wani dan jihar nasarorin Tinubu da kyawawan shirin da yake yiwa kasar, rahoton Vanguard.
Source:legithausang