Kungiyoyin kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Adamawa ta bi sahun mambobin kungiyar a kasa baki-daya, wajan shiga zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya, tare da kira ga gwamnatin da ta duba yanayin da talakawar kasar ke ciki.
Kwamared Emmanuel Fashe, shi ne shugaban kungiyar ya yi kiran a Yola, ya ce gwamnatin tarayya ta sassauta manufofinta, domin kuwa ‘yan Nijeriya na cikin wahalar da ba za’a iya kwatantashi ba.
Da yake karbar wasika a madadin gwamnatin jihar ta Adamawa shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Dakta Edgar Amos Sunday, ya bada tabbacin ma’aikatan na yin duk mai yiwuwa don ganin an magance wahalhalun da al’ummar jihar Adamawa ke ciki.
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin ya kuma yabawa kungiyar kwadagon bisa yadda su ka gudanar da zanga-zangar bisa tsari, kwanciyar hankali da lumana.
Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta ce ta kammala shirye-shiryen yaye dalibai 11,000 karo na 38 a tarihin Jami’ar.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Abbas ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Kano.
Duba Nan: Karrama Wasu Mutane. Jami’ar Bayero Kano
Abbas ya ce, a yayin bikin, dalibai 180 sun kammala karatun digiri da daraja ta daya, 3,770 sun kammala karatun digiri na biyu (Masters), sai kuma dalibai 370 da suka kammala digiri na uku.