Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewar adadin mutane da dama ne suka mutu cikin su harda Magajin Garin Banibangou sakamakon harin da ‘Yan ta’adda suka kai Yankin Tillaberi dake kusa da iyakar kasar Mali da Burkina Faso.
Wani dan majalisa daga Yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewar Magajin Garin Banibangou na daga cikin wadanda aka kashe, kuma an samu gawar sa.
Wannan na daga cikin munanan hare haren da ‘Yan ta’adda ke kaiwa wasu sassan Jamhuriyar Nijar, musamman kusa da iyakar Mali.
Ya zuwa wannan lokaci hukumomin Nijar basu fitar da sanarwa akan adadin da da wannan kazamin harin ya rutsa dasu ba.
A wani labari na daban majiyoyin tsaro a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da wani harin mayaka masu ikirarin jihadi da ya hallaka fararen hula 10 lokacin da su ke tsaka da sallah a wani kauye na jihar Tillaberi da ke yammacin kasar gab da kan iyaka.
Kauyukan jihar Tlaberi da ke gab da kan iyakar Jamhuriyyar Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso masu fama da hare-haren kungiyoyin da ke ikirarin jihadi, su ne kan gaba yanzu haka a kasar ta yankin Sahel a jerin yankunan da ke fuskantar tashe-tashen hankula.
Wani jami’i a garin Banibangou ya shaida wa kamfanin dilancin labaran Faransa cewa maharan bisa babura sun isa garin ne a yayin da ake tsaka da sallar magriba, inda suka iske wadanda abin ya rutsa da su a masallaci.
Batun yaune aka fara samun kungiyoyin masu alaka da wahabiyanci su kai hari kan mutane ba a kasar.