Abin Da Yasa Buhari Baya Raba Wa Mutane Kuɗi_Mashawarcin Buhari.
Mashawarci na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari Femi Adesina ya ce mai gidansa ya gwammace ya kashe kudi wurin taimakawa talakawa da marasa galihu a maimakon bada kudin domin a yi masa alfarma.
Adesina ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis mai lakabin, ‘Buhari’s Kind of Kindness’.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce jajircewa wurin hidimtawa talakawa da kaunar da ya ke yi wa marasa galihu ya sa ya yi nasara a zaben 2015 ya kuma zarce a 2019.
Ya ce a maimakon bada toshiyar baki ko cin hanci, Buhari ya gwammace ya yi amfani da kudin domin tallafawa mutane mabukata a sassan kasar nan. “Buhari ba zai baka buhun kudi ba domin ka masa alfarma ba.
A maimakon hakan, zai bada kudin ne domin yin ayyukan alheri, jin kan marasa galihu da talakawa da mabukata,” ya rubuta. Hakazalika, Adesina ya bayyana maigidansa a matsayin ‘mutum mai tausayin talakawa, gajiyayyu da marasa galihu.’
Wani sashi na rubutun ya ce, “Yana kaunar su sosai, kuma suma suna sonsa sosai. Wannan shine Shugaba Muhammadu Buhari.
“A kan ce mutumin yana da kuri’u a kalla miliyan 12 suna jiransa a sassa daban-daban na kasar tun kafin a fara kada kuri’a a babban zabe. “Talakawa da marasa galihu sune suka fi yawa cikin masu kada kuri’a. Suna taruwa a wurinsa kamar yadda zuma ke taruwa a gidansu.”
Adesina ya kuma ce irin wannan tausayin ta talakawa ne yasa Buhari ya kafa Ma’aikatar Jin Kai, ya kuma nada Sadiya Umar Farouq a matsayin jagora.
Domin a cigaba da taimakawa talakawa, hakan yasa talakawa ke son Buhari domin ya damu da matsalolinsu kuma a kullum yana tunanin yadda zai tallafa musu.