Kungiyar Abia Christian Community (ACC) za ta fadawa mabiyanta ‘yan takaran da za a zaba.
Gamayyar kiristocin za ta goyi bayan jam’iyyar NNPP a zaben Gwamna da za a shirya a Abia.
Shugaban ACC ya ce Dr. Ukpai Iro Ukpai shi ne wanda suke tare da shi a zaben kujerar Gwamna.
Wata kungiya ta gamayyar kiristoci a jihar Abia, Abia Christian Community (ACC), ta tsaida ‘yan takaran da za ta goyi bayansu a zaben 2023.
This Day ta ce kungiyar addinin ta fito da duka ‘yan takaran da suka cancanta su zaba, ba tare da la’akari da jam’iyyar da ‘dan siyasa ke neman mulki ba.
A karkashin kungiyar ta Abia Christian Community, akwai kungiyoyi irinsu NGCF, APNET da MKM da za su taimaka wajen kawo cigaba a jihar Abia.
Daga cikin ‘yan takaran da suka samu goyon bayan ACC akwai Dr. Ukpai Iro Ukpai mai neman zama Gwamna a zabe mai zuwa a karkashi inuwar NNPP.
Dr. Ukpai Iro Ukpai shi ne wanda kungiyar za ta goyi baya a zaben Gwamna da za a shirya.
Sauran ‘yan takaran da za su samu tabarrukin Abia Christian Community za su fito ne daga wasu jam’iyyun siyasan dabam da NNPP mai alamar kayan dadi.
‘Kafintocin Abia 2023’ Wadanda ACC za ta marawa baya a zaben kujerar Sanatoci, majalisar wakilan tarayya da majalisar dokoki za su fito daga APC, PDP, da makamantansu.
Shugaban kungiyar kiristocin, Apostle Reminder C. Gad ya kira wadannan ‘yan siyasa da za su zuba da ‘Kafintocin Abia 2023’, ma’ana masu yin gyara.
Reminder C. Gad ya ce kungiyarsu ba ta siyasa ba ce, an rahoto shi yana cewa an kafa ta ne domin ganin an samu shugabanci na gari da zai amfanar da jama’a.
Dr. Ukpai Iro Ukpai wanda kungiyar ta tsaida a matsayin ‘dan takaranta a zaben Gwamna, ya yi jawabin godiya na goyon bayan da ya samu a yau.
‘Dan takaran Gwamnan ya yi kira ga Abia su tashi tsaye a 2023 wajen ganin an samu shugabanni na kwarai, yanzu ita ce jihar da ta fi rashin dacen shugabanni, Shinkafa ta gagara Buhun shinkafa ya yi tsada a kasuwa, ya gagari Gwamnati, an ji labari Gwamnan Anambra ya soke rabon shinkafar kirismeti da aka saba yi a duk shekara.
Bayan karin albashi, Gwamnatin Farfesa Chukwuma Charles Soludo za ta ba duk wani ma’aikaci N15, 000 domin ayi shagalin kirismetin shekarar nan.