An dakatar da yan takarar gwamna a jihohi hudu a Najeriya na jam’iyyar AAC sabida wasu dalilai.
A wani rahoto da ya bazu ranar Talata, jam’iyyar ta dakatar da masu neman zama gwamna a Taraba, Kwara, Akwa Ibom da Enugu.
An zargi ‘yan siyasan da saba kundin jam’iyya kuma sun gaza kare kansu kan tuhumar da ake masu.
Jam’iyyar African Action Congress (AAC) ta dakatar da masu neman zama gwamna hudu a jihohi daban-daban yayin da ya rage kwanaki kasa da 60 zaben 2023.
Jaridar Sahara Reporters ta rahoto cewa jam’iyyar ta dakatar da ‘yan takarar ne bisa kama su da saba wa dokokin kwansutushin ɗin da aka kafa AAC a kai.
‘Yan takarar da lamarin dakatarwan ya shafa sun hada da, Iboro Ofu na jihar Akwa Ibom, Ray Kene na jihar Enugu, David Joel Charima, na jihar Taraba da Ahmed Aliyu na jihar Kwara.
Jam’iyar AAC reshen jihar Akwa Ibom tace abun takaici ne kasancewar Otu ya gaza kare kansa game da tuhumar da jam’iyyar ta masa.
Bisa haka kwamitin zartaswa na Akwa Ibom ya yanke shawarin dakatar da dan takarar gwamnan ba tare da bata lokaci ba.
Haka zalika, Usman Jamiu, shugaban APC a jihar Kwara, a wata sanarwa ya ce Aliyu ya yi fatali da tuhumar da aka masa ya ki kare kansa kuma jam’iyyar ta ci gaba da daga masa kafa duk da wa’adi ya cika amma shiru.
Sakamakon haka kwamitin zartaswa ya kafa hujja da sashi na 81 sakin layi na 3, wanda ya yi daidai da sashi na 81 sakin layi na 2 (a) na kwansutushin ɗin AAC wanda ya shawarci a kori dan takarar gwamna.
Sanarwan ta ce: “Saboda haka muna ba ka shawarin ka dakatar da duk wata mu’amala a madadin jam’iyyar AAC domin ba zamu sake daukar nauyin kare ka ba.”
Hadimin Atiku Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Mutane Uku Hakuri Kan Kalamansa
A wani labarin kuma Rigingimun jam’iyar PDP na kara tsananta bayan Wike ya sake fallasa wata manaƙisar Atiku tun a 2023.
Sai dai lamarin bai yi wa makusantan Atiku dadi ba, inda aka ji Phrank Shaibu ya fito yana neman Wike ya baiwa mutane uku hakuri tun da wuri.
Wike da sauran mambobin tawagarsa na G-5 sun kafe kan bakatarsu wacce har yanzun babu alamun za’a iya biya masu ita a PDP.