Tsohon gwamnan Kano Shekarau ya amince ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP kuma Atiku da kansa zai karɓe shi yau Lahadi.
Shugaban PDP, Shehu Wada Sagagi, ya ce shirye-shirye sun yi nisa na zuwan Atiku da kuma dawowar Malam Ibrahim Shekarau.
Sanata Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya ya raba gari da NNPP ne bayan gaza baiwa mutanensa tikitin takara a 2023.
Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa zai ziyarci jihar Kano ranar Lahadi (yau) domin karɓan Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau zuwa jam’iyyar PDP.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Shekarau ya fice daga PDP zuwa APC ne yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2019 da ya gabata.
A halin yanzu, ya samu saɓani da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, hakan ta sa ya koma NNPP mai kayan marmari.
Sai dai watanni kalilan bayan sauya shekar Shekarau zuwa sabuwar jam’iyyar, alaƙarsa ta yi tsami da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso bayan mutanen Sanatan ba su samu tikitin takara ba kamar yadda aka musu alƙawari.
Sanatan ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, inda ya masa tayin muƙamai masu gwabi kuma daga bisani ya gana da Bola Tinubu, mai neman gaje Buhari a APC.
Tsohon gwamanan na kan hanyar komawa jam’iyyar PDP, domin wata majiya ta tabbbatar da cewa shirye-shirye sun kammalu wajen ganin Shekarau ya ƙara karfin tawagar Kanfen ɗin Atiku a Kano. Shekarau ya amince ya dawo PDP – Sagagi.
Da yake jawabi ga jaridar Dailytrust, shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa Shekarau ya amince ya dawo jam’iyyar hammayya PDP.
Ya ce: “Mun gode Allah, daga karshe mun samu jagora a jihar Kano kuma na ji daɗin haka.
Shekarau, kasancewarsa mai rike da babban ofishin siyasa, ya amince kuma muna masa maraba da dawo wa jam’iyyar mu PDP.”
“Shirye-shirye sun yi nisa na karɓan baƙuncin Atiku Abubakar, wanda zai ziyarci Kano ranar Lahadi, muna fatan shi zai karɓi tuban Malam Shekarau.
Mun yarda mu masa biyayya kuma nasara ta mu ce da ikon Allah.”
A wani labarin kuma Ministar jin kai da walwala ta ce da ikon Allah Mijinta ne zai lashe zaɓen gwamnan Bauchi a 2023.
Ministar harkokin jin kai da walwala, Hajiya Sadiya Farouq, ta ce idan Allah ya so mijinta ne gwamnan jihar Bauchi na gaba a 2023.
Hajiya Sadiya, Minista mafi karancin shekaru a gwamnatin Buhari, ta ce Sadique Abubakar mutum ne da kowa zai so ya zama gwamna.
Source: LEGITHAUSA