Masu amfani da kafafen sada zumunta sun nuna mamaki kan bidiyon wani dan Najeriya da ke tafiya akan kiras din kwai.
Duk da yadda ya saki nauyinsa akan kiras din, babu ko daya a cikin kwan da ya fashe kuma haka ya janyo muhawara akan bidiyon.
Matashin ya na shirya kiras din ne a motar daukar kaya kuma ya zama sai ya taka kwan kafin ya jera.
Abu ne sananne cewa kwai ba shi da kwari kuma zai iya fashewa idan ya ji matsi.
Sai dai, wani bidiyo ya janyo cece-kuce a yanar gizo akan rashin kwarin kwai.
Bidiyon ya nuna wani yadda wani matashi dan Najeriya ke hawa lodin kiras yana tsani da su.
Wannan matashi ya ketare iyakar kimiyya bayan da masu amfani da kafafen sada zumunta su ka fara dawo da abun da suka koya a makaranta kan dalilin da ya hana kwan fashewa.
Ya jera kiras din kwai daga gidan gona zuwa motar daukar kaya da zata raba su wurare.
Bidiyon ya nuna yadda ya ke rike da wasu kiras din ya na tafiya zuwa inda motar ta ke.
Daga nan, sai ya hau bayan motar ya kuma hau kan shiryayayyun kiras layi biyu don ajiye wanda ya dauko. Kwata kwata kwan bai fashe ba yayin da ya ke tafiya.