Wani mai suna Theo ya jika zukatan al’umma yayin da ya dawo wurin matar da ya taba yi mata sata shekarun da su wuce.
Ya ziyarci shagonta, inda ya sayi kayayyaki kafin daga bisani ya bayyana mata laifin da ya taba aikata mata a baya.
Kamar ba komai ba, haka ya dauki wasu adadin kudade masu yawa ya damka mata tare da gode mata.
Wani dan Najeriya ya jika zuciyar wata mata yayin da ya gwangwaje ta da kyautar N100,000 a madadin mayar mata da kayan da ya sace mata a shekarun baya.
Mutumin mai suna Theo Ayomoh ya ziyarci shagon matar, inda ya sayi biskit tare da cewa, a nan ya taba satar alawa.
Daga nan, ya gabar da kansa, inda yace a lokacin yana yaro ta taba kama shi lokacin da ya yi mata satan alawa, bai wuce shekaru takwas ba.
Ya kuma bayyana cewa, ba wancan karon bane na farko da ya yi mata sata, kawai dai ta yi nasarar kame shi ne a wancan ranan. Lokacin da matashin ya zo shagon matar.
Theo ya nuna godiya da kuma yaba mata bisa koya masa hali mai kyau na hana shi sata da kuma kin fada wa iyayensa. Musamman ya durkusa a kasa don gode mata.
Wannan ya faru ne bayan da ya dauko kudi N100,000 ya ba ta tare da kalaman godiya. Matar ta shiga mamaki da ganin wannan rana.