Soyayya bata tsufa sai dai ma’abota yinta su tsufa kamar yadda masu hikimar zance ke fadi Wasu ma’aurata yan kasar Indiya biyu sun tsufa sosai amma basu daina nunawa junansu kulawa ba.
A cikin wani bidiyo da ya yadu, an gano tsohon magidancin yana rikewa matarsa lema cike da soyayya da kauna yayin da ake zuba ruwan sama.
Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyana bidiyon wasu tsoffin ma’aurata biyu wanda ke nuna lallai sun sha soyayya a zamanin kuruciya.
A cikin bidiyon da shafin theotherelement ya wallafa a Instagram, an gano ma’auratan biyu wadanda suka tsufa tukuf-tukuf suna tafiya yayin da ake zuba ruwan sama.
An kuma gano mijin rike lema yana bin matar tasa cike da kulawa a kokarinsa na tabbatar da ganin cewa ruwan bai taba ta ba.
Hakazalika, mutanen da ke wajen na ta kallonsu cike da sha’awa.
Martanin jama’a:
the_endless_ever ta yi martani: “Wasu alkawaran na har abada ne ❤” worldisee.bymehakgarg ta ce: “Irin wannan idiyo mai matukar kyau! ” ajay.pawar_0001
“Soyayya na hakika ” harshaliiii17 ta yi martani: “Sun yi kyau matuka❤️”
Yadda Wata Amarya Da Kawayenta Suka Yi Shiga Ta Kamala, Bidiyon Ya Burge Mutane A wani labarin kuma, kamar yadda yake kasancewa a tsakanin amare da yan matan amare na wannan zamani, idan aka ce bikin waninsu ya tashi sukan yi shiga ta kece raini.
Hakazalika, wasu kan yi shiga ta nuna tsaraici duk don nuna cewa sun waye da kuma son ganin hankula sun karkata a kansu. Sai dai wata amarya da kawayenta sun sauya tunani inda suka yi shiga ta kamala a yayin shagalin bikin kawar tasu.
Source:legithausang