Wata amarya ta janyo cece-kuce a wajen ɗaurin auren ta bayan ta ƙi yarda angonta ya rungume ta.
Amaryar ta naɗe hannayenta sannan ta ɗaure fuska lokacin da angon ya miƙa hannayen sa yana son ya rungume ta.
Bidiyon wanda ya yaɗu sosai ya janyo cece-kuce, inda wasu da yawa suke cewa auren dole ne aka yi mata.
Wani bidiyo da ya yaɗu na wani wajen ɗaurin aure ya nuna lokacin da wata amarya ta ƙi yarda ta rungume angon ta.
Amaryar wacce ba ta cikin farin ciki ta ƙi yarda angon ya rungume ta inda ta maƙale hannayen ta lokacin da ya ke ƙoƙarin rungumo ta. Amarya ta ki yarda angonta ya rungume ta.
Ganin cewa ba za ta yarda ya rungume ta ba, sai angon ya matsa kusa da ita inda ya rungumo ta da ƙarfin tsiya, sannan ya haɗa mata da sumbata.
Duk da haka dai amargar ta ƙi sakin fuska ta yi murmushi. Bakin da suka halarci wajen sun kewaye su da kyamarori suna ɗaukar abinda ke wakana.