Kotu ta bada umurnin a tura mawakin gambara na Najeriya, Panshak Zamani wanda aka fi sani da Ice Prince zamani gidan gyran hali.
Hakan na zuwa ne bayan kama shi da yan sanda suka yi kan dukkan dan sanda da barazanar jefa shi a rafi lokacin da aka tare shi yana tuki babu lamba .
Alkalin kotun, amma, ya bada belin mawakin kan kudi N500,000 da mutum biyu tsayayyu da za su karbe shi idan ya cika sharrudan.
An tsare fitaccen mawakin gambara na Najeriya, Panshak Zamani wanda aka fi sani da Ice Prince Zamani a gidan yarin Ikoyi.
Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Legas, ya shaidawa Premium Times cewa an gurfanar da mawakin a kotun majistare da ke Ajah a ranar Juma’a.
An gurfanar da shi kan tuhume-tuhume uku masu alaka da duka, sace mutum da hana hukuma aikinta.
Dukkan Dan Sanda Hundeyin, cikin sanarwar da ya fitar a Twitter ya ce an kama mawakin.
Ya ce an kama Ice Prince ne kan dukkan dan sanda da ya tsare shi saboda yana tuki ba tare da lamba ba a motar.
A sakon da ya wallafa a Twitter, Mista Hundeyin ya ce mawakin ya yi barazanar zai jefa dan sandan a cikin rafi a lokacin da aka kama shi.
Dan sandan ya wallafa hoton mawakin da ankwa a hannunsa yana mai cewa za a gurfanar da shi a kotu.
Beli Mr Hundeyin ya shaidawa Premium Times cewa an bada belin wanda ake zargin kan sharuddan biyan N500,000 tare da masu tsaya masu guda biyu.
Ya kara da cewa za a saki mawaki da zarar ya cika sharrudan belin. An dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Satumba.
Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Umurci Mawaki Portable Ya Kai Kansa Ofishinta Ko Ta Kamo Shi.
A wani rahoton, Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Ogun ta umurci fitaccen mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya kai kansa ofishinsu mafi kusa nan take ko kuma a kama shi.
Hakan ya biyo bayan zargin duka da aka ce ya yi wa tsohon DJ dinsa mai suna DJ Chicken, rahoton Daily Trust.
A wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Portable, wanda ya yi magana da harshen Yarbanci ya umurci yaransa su yi wa DJ Chicken duka kan zargin ya tura wa matarsa sako.
Sourcce:legithausang