Kungiyar kasashe masu arzikin mai OPEC ta ce Najeriya da sauran kasashe masu tasowa za su amfana da kimanin dalar Amurka biliyan 450 da za a kashe wajen gina sabbin matatun mai da kuma bunkasa ayyukan wadanda suke da su.
OPEC ta ce zuba jarin wani bangare a karkashin gagarumin shirin da take jagoranta, da ya kunshi dala tiriliyan 1 da biliyan 500, da za a zuba a bangaren mai da iskar gas domin bunkasa fanonin daga 2021 da muke ciki zuwa shekarar 2045.
A wani labarin na daban kuma cacar bakan da ta barke tsakanin Saudiya Hadaddiyar Daular Larabawa ta tilasta dage taron da aka fara a ranar Litinin na kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC wanda najeriya na daya daga cikin su, da kuma kawayenta kan shirin daukar matakin rage hauhawar farashin danyen mai a duniya.
Tun cikin watan Mayun da ya gabata kasashen 23 masu arzikin danyen mai na ciki da wajen kungiyar OPEC ke kara yawan danyen man da suke hakowa da kadan kadan, bayan zaftare shi da suka yi a shekarar bara, saboda mummunar fadowar da farashinsa yayi a dalilin barkewar cutar Korona.
Kudirin bayan bayan nan da kasar Daular Larabawa ta hau kujerar naki akai shi ne na kara yawan danyen man da kungiyar OPEC da kawayenta ke hakowa duk rana da adadin ganguna dubu 400 duk wata daga Agustan dake tafe har zuwa karshen shekarar nan da muke, adadin da zai kai ganga miliyan 2 kenan a kowace rana.