Jama’a sun yi ta cece-kuce bayan ganin wani kalan daukar hoto na wasu ma’aurata; mata biyu da mijinsu daya.
An ga masoyan na cin duniyarsu da tsike a cikin kaya iri daya, ga kuma mijin na kwance a kan cinyoyin matansa biyu.
Kishin wasu mata ya tashi a kafar sada zumunta, wasu kuma suka ce ba za su taba iya auren namijin da ke da mata ba.
Wasu hotuna sun yadu a kafar sada zumunta na yadda wani magidanci yake shan soyayya daga matansa kyawawa, lamarin da ya jawo cece-kuce.
Mutumin da ba a gano waye shi ya sanya kaya iri daya da matansa biyu, inda suka dauki hotuna masu daukar hankali.
A daya daga cikin hotunan da aka yada a TikTok, mutumin ya kwanta a kan cinyoyin matansa biyu kamar karamin yaro.
A sauran hotunan kuwa, yana sumbatarsu a baki.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kafar sada zumunta ta dauki dumi, mutane sama da miliyan 4 ne suka kalli hotunan da ke cike da cece-kuce.
Martanin jama’a Mutane da yawa sun bayyana abin da suka ji da ganin wadannan hotunan masu daukar hankali, ga kadan daga ciki: @Call-mi-Diva: “Babu wanda naga yana magana game da hoto na ukun.”