Nigeria Da yake zantawa da BBC Hausa ranar Lahadi, daraktan shirin wanda shine shugaban sashin wasan kwaikwayo na Arewa24, yace ya zama wajibi su cire ta saboda uzurin da jarumar ta bayar.
Wani abu da ya ɗaure wa masu bibiyar shiri mai dogon zango, Kwana Casa’in, kai shine zare Salma, diyar tsohon gwamna Bawa Maikada Daraktan shirin, Salisu T Balarabe,
ya bayyana ainihin abinda yasa suka cire jarumar daga cikin shiri zango na 6 Yace Salma da kanta tace ba zata cigaba da fitowa a shirin ba saboda wani abu da ta alakanta shi da mahaifanta.
Kano – Mai bada umarni a shiri mai dogon zango, Kwana Casa’in, Salisu T Balarabe, ya bayyana dalilin zare jaruma a cikin shirin, Maryuda Yusuf, wacce aka fi sani da Salma.
Dailytrust tace Salma dake taka rawar ɗiyar tsohon gwamnan jihar Alfawa a cikin shirin, Bawa Maikada, ta shahara bisa matsayin da ta fito da halayyarta a shirin.
Jarumar tana yaƙi da ayyukan cin hanci da rasahawa na iyayenta, kuma tana soyayya da Sahabi, wanda suka ɗauka a matsayin makiyinsu, duk a cikin shirin Kwana Casa’in.
Sai dai masu kallon shirin sun nuna matukar mamakin su, kasancewar ba su ga jarumar ba a zango na 60, wanda a baya-bayan nan tashar Arewa24 ta fara haska wa.
Meyasa suka cire Salma?
Da yake zantawa da BBC Hausa ranar Lahadi, daraktan shirin wanda shine shugaban sashin wasan kwaikwayo na Arewa24, yace ya zama wajibi su cire ta saboda uzurin da jarumar ta bayar.
Yace:
“A tsarin tashar Arewa24 duk lokacin da za’a ɗauki wani zango, akan sanar da jaruman shirin cewa an saka ranar cigaba da ɗaukar wani zango. Waɗan su kan bada uzurin cewa ba zasu samu damar yi ba saboda karatu ko wani abu.”
“Yayin da muka tuntubi Salma kan ɗaukar shirin Kwana Casa’in Zango na 6, ta faɗa mana ba zata samu damar yi ba.” “Mun nemi ta faɗa mana dalili amma sai tace yana da alaƙa da iyayen ta kuma ba lallai bane ta iya bayyana mana ba.”
Kalubale da nasarorin da muka samu a Kwana Casa’in
A cewar Balarabe, sun sha fama da kalubale kala daban-daban tun bayan fara nuna shirin, musamman daga yan siyasa da jami’an gwamnati, inda suke tunanin da su ake.
A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood.
Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam Zamgo, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau.