1. Sunanta na gaskiya, Hilda Bassey Effiong, matashiya ce mai dafa abinci a Nijeriya daga Karamar Hukumar Nsit Ubium ta jihar Akwa Ibom, Tana da wurin dafa abinci a Legas mai suna “My Food by Hilda”
2. Zata yi girki na tsawon kwanaki 4 ba tsayawa.
3. Cikin sharudan gasar dole ta tsaya ta yi girki na tsawon lokaci a tsaya ba tare da ta zauna yayin girkin ba.
4. Ba a yarda ta sha kofi ko abubuwan kara kuzari, ko wani abin sha don kara karfin jikin yayin dafa abinci.
5. An ba ta damar cin abinci, shan ruwa ko ruwan ‘ya’yan itace, da shan glucose.
6. Ana yin gasar girkin ne a wurin shakatawa na ‘Amore Gardens’ da ke Lekki, Jihar Legas, Nijeriya.
7. Tana yin girki safe da dare da rana na tsawon darare 4 ba tare da yin barci ba.
8. Tana da hutun mintuna 5 kacal a kowace awa [ma’ana kowane awa 1, tana da hakkin ta huta na mintuna 5 kacal, wato hutun sa’a a kowane awa 12].
Wasu majiyoyi sun ce
Tana samun hutun mintuna 30 duk bayan sa’o’i 6, tana kwashe mintuna 30 a cikin motar asibiti da ke kusa da ita, inda za ta iya yin barci, ta yi amfani da dakin wanka, sannan ta sami tantancewar likita ko duba lafiyar ta daga tawagar likitoci.
9. Duk abin da ta dafa tana raba wa mutanen da ke wurin kyauta ba tare da sayar da abincin ba.
10. Takan dafa abinci daban-daban lokaci guda. Tana da ‘yancin dafa duk abincin da take so. Babu takurawa kan girkin da ta iya da wanda ba ta iya ba. Taken shiga gasar ta duniya shi ne ‘Dafa abinci cikin ƙayyadadjen lokaci’.
11. Kowane abinci da aka dafa da kowane farantin da aka ba da shi ana rubuta shi. Ta dafa abinci sama da kala 115 kawo yanzu.
12. Ta fara girkin ne a ranar Alhamis kuma ana sa ran za ta kammala lokacin da aka yi niyya zuwa ranar Litinin 15 ga Mayu, 2023 da yamma.