Hukumar Watsa Labarai ta kasa ta dira kan Ado Gwanja, ta haramtawa gidajen rediyo sanya wakar sa.
A makwannin da suka gabata ne malamai da sauran jama’ar gari suka yi ta cece-kuce kan wakar Gwanja mai suna Warr.
Ana yawan samun rikice-rikice da mawakan Hausa a Arewacin Najeriya bisa aron al’adun da basu dace ba.
Makwannin da suka gabata ne kafafen sada zumunta a Arewacin Najeriya suka dauki dumi yayin da wani mawakin Hausa, Ado Gwanja ya saki wata waka mai cike da maganganun da suka saba al’ada.
Malamai da masu tsokaci sun yi ca kan wakokin ‘Warr’ da ‘A Sosa’, inda suka zargi Gwanjo da kawo wani sabon salon bata tarbiyya da kawo tsaiko ga al’adar Mallam Bahaushe.
Bayan cece-kuce da koke daga malamai da masu sharhin lamurran yau da kullum, gwamnati ta bayyana daukar mataki kan gidajen rediyo dake yada wakar.
A wata sanarwa da Hukumar Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta fitar, ya bayyana bukatar cewa, ya kamata gidajen rediyo suke kallon tsanaki kafin fara sanya wakoki a kafafensu.
Sanarwar ta ce, labari ya iso hukumar cewa, akwai gidajen rediyon dake sanya wakar ‘Warr’, don haka ta bukaci a dakata da hakan tare da gudun irin wadannan wakoki masu bata tarbiyya da kuma nuna alamar marisa daga buguwa.
A cewar hukumar, ci gaba da sanya wakar da makamanciyarta sun saba sashe na 3.18.1 (c) da 3.9 na kudin tsarin hukumar watsa labarai ta kasa.
Idan baku manta ba, a makon nan ne aka tashi da labarin cewa, hukumomi da daidaikun mutane sun maka Gwanja da wasu mawakan da ke irin wadannan wakokin a kotu, inda tuni aka mika musu sammaci.
A wani labarin, an yi karar wasu mawakan gambara na arewa da masu fada a ji a TikTok a babban kotun shari’a da ke Bichi, Kano kan aikata abubuwan ‘gurbata tarbiyya’.
Duk da cewa ba a samu ganin kwafin takardar karar da aka shigar ba, majiya da ke da masaniya kan lamarin ta shaida wa Daily Nigerian cewa laifin na da alaka da wakoki da bidiyon TikTok da ka iya lalata tarbiyar al’umma.
Amma Daily Nigerian ta samu kwafin wasikar da kotun shari’ar ta rubuta wa rundunar yan sanda inda ta bukaci ta yi bincike kan koken da mai shigar da karar ya yi.
Source: LEGITHAUSA