Yan Najeriya da dama suna caccaki Fasto David Ibiyeomie na cocin Salvation Ministries Ku tuna cewa a kwanan nan ne.
Ibiyeomie ya hana ma’aurata yin tarayya da junansu na tsawon kwanaki 21 yayin da cocin ya fara azumi.
Da suke martani, yan Najeriya sun ce wannan umurni baya cikin littafi mai tsarki kuma ko da zai yi aiki a kan marasa aure ne.
Ba sabon labari bane cewa babban faston cocin Salvation Ministries da ke Port Harcourt, Fasto David Ibiyeomie, ya hana ma’aurata kwanciyar aure na tsawon kwanaki 21 yayin da cocin ya shiga azumi da addu’a.
Da suke martani ga hakan, yan Najeriya da dama sun yi ikirarin cewa dalilansa basa da hurumi a cikin littafi mai tsarki.
A cewarsu, kamata ya yi ace wannan doka zai yi aiki ne a kan marasa aure.
A Ina Aka Fadi Haka?
Ibiyeomie ya ce: “Ku kauracewa mu’amalar aure a wannan lokaci na azumi saboda na ji mutane na cewa ‘mijina ya ce da zaran mun sha ruwa tunda mun ci abinci, mu ci wannan ma’! Don haka, na ji wannan!
A matsayina na Fasto, sun ce mani dan Allah ka yiwa mijina magana cewa muna azumi!
“Kwanaki 21 ba zai kashe ku ba!’ Ku guji zuwa wannan bangaren! Rayuwa ba a kansa bane.
Yanzu ba lokaci ne na kwanciya da mazaje da matayenku ba! Kun ji abun da nake fadi?
Daga gobe ku rufe wannan wajen har sai bayan kwana ashirin da daya!”
Ga martanin wasu yan Najeriya Adaora Clara Sommie Anyim: “Amma Allah ne ya yi umurnin ayi aure.
Kamata ya yi ace wannan umurni ya yi aiki a kan marasa aure.
Ina ganin ya kamata mutane su daina zakewa a kan wasu abubuwa.
Irin wanna umurnin zai kawo matsaloli a wasu auren.
Wanda ake magana a kai miji/matarka ce, ba daduro ba.
Allah ya halasta kwaciyar aure ga ma’aurata kawai.
Juliet Onyekachi: “Abuj da Allah ya hada, kada a bari mutum ya kawo tangarda da irin wannan yanayi…
Ba zai hana ku yin addu’o’inku ba..kawai ku yi amfani da wannan kwanaki 21 ku chanja munanan dabi’unku, ku taimakawa mabukata sannan ku yada soyayya a tsakani.
Wannan shine abun da Allah yake kallo ba abun da kuke yi da abokan zamanku ba.”
Ngobua Nora Nabem: “Ban gane ba wato idan mutum na azumi laifi ne ya kwanta da matarsa ta sunna ko miji?”
PJ More: “Ba ka da kowani yanci na hana ma’aurata sauke hakokinsu na aure.”
A wani labari na daban, wasu ma’aurata da suka kwashe tsawon shekaru 13 tare harda yara biyu sun gano akwai alaka ta jini a tsakaninsu.
Kamar yadda suka bayyana a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, sun gano cewa su din yaya da kanwa ne.