Wata yarinya mai suna wasilat yar Najeriya da aka haifa da idanu na musamman ta yi fice a intanet kuma mutane sun mato a kanta.
An haifi yarinyar mai shekaru 7 da idanu mai launin shudi da kyalli kuma ita kadai ke da irin shi a gidansu gaba daya.
Hotunan ta sun sburge masu amfani da soshiyal midiya amma wasu na ganin akwai wani al’amari tattare da kamanninta.
Wata yarinyar mai shekaru 7 da aka ambata da suna Wasilat ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya saboda yanayin idon da Allah ya halicceta da shi.
Tima Wire ta ci karo da kyakkyawar yarinyar sannan ta wallafa hotunanta a shafin Facebook na Rant HQ Extention bayan ta matukar burge ta.
“Wow yarinyar da na hadu da ita a yau tana da matukar kyau da kwayan idanunta,” Tima ta rubuta yayin da ta wallafa hotunan yarinyar.”
A ranar 31 ga watan Disamba, Tima ta sake wata wallafa da yarinyar a shafin inda ta dungi yabon kwayoyin idanun Wasilat.
Tima ta bayyana cewa sabanin abun da mutane da dama ke hasashe cewa yarinyar ta yi amfani da kwayar idon bogi ne, haka Allah ya halicce ta.
Lokacin da Legit.ng ta tuntube ta, Tima ta bayyana cewa ta hadu da Wasilat ne a kauyen mahaifiyarta.
“Sunanta Wasilat koda dai bata da wani alaka da ni kawai dai na hadu da ita ne a kauyen mahaifiyata sai na yanke shawarar daukarta hoto sannan na saki hotunan don ganin ikon Allah.”
Tima ta kara da cewar ta tabbatar ance daga Kogi take cewa wannan ba cuta bane, amma cewa an haifeta ne a haka.
“Shekarunta 7 kuma ita kadai ce da irin shi a gidansu. Daga jihar Kogi take kuma da shi aka haife ta.”
Ben Sigie ya ce: “Yar baiwa.” Quin Ria ta ce: “Ita din ta daban ce.” Echero Favour ta ce: “Idanunta na da kyau amma yana iya shafar jinta a gaba amma muna rokon kada Allah yasa hakan ya faru.”
Peace Njoku ta ce: “Dubi idanun da nake kashewa kudina. Rayuwar nan ba sauki.”
Budurwa ta ginawa iyayenta dankareren gida
A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta gwangwaje iyayenta da wani hadadden gida na kerewa sa’a.
Kamar yadda budurwar ta bayyana, ta jima tana mafarkin cika wannan buri nata na yiwa mahaifanta abu na musamman.