Tsohuwar matar jarumi Adam A. Zango, tsohuwar jaruma Maryam AB Yola, tayi aure babu zato balle tsammani da kyakyawan angon ta.
A bidiyoyin da ta zuba a shafinta na Instagram, jarumar ta bayyana cike da farin ciki inda ta dinga rawa cike da so da kaunar angonta Muhammad.
Tuni dai tsofaffin abokan sana’arta da masoyanta suka dinga tururuwar yi mata addu’a da fatan zaman lafiya yayin da ta shiga daga ciki.
Tsohuwar matar fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, Maryam AB Yola ta yi auren ba-zata a ranar Juma’a da ta gabata.
Kamar yadda jarumar da kanta ta wallafa bidiyoyinta tare da kyakyawan angonta a shafinta na Instagram mai suna @ab_yola_beauty_skin_care, ta sanar da masoyanta cewa a yanzu fa ta zama matar Muhammad.
Hoto daga @ab_yola_beauty_skin_care.
A ranar Juma’a da yammaci ta daura wani bidiyonta ta sha lalle sanye da kayan amare.
Kallon bidiyon ga duk wanda ya saba bibiyarta a shafinta na Instagram, za a iya cewa iya adonta ne da ta saba don dama can ‘yar kwalisa ce.
Sai dai ba kwalisar bace kadai, ashe shigewa tayi daga ciki. Tsokacin da tayi a kasan bidiyon ne ya fallasa hakan. Ta rubuta: “Alhamdulillah ala kulli halin! Mrs Mohammad.”
Babu dadewa kuwa tsofaffin abokan sana’arta, suka dinga tururuwar yi mata Allah sam barka tare da fatan alheri.
Kyakyawar amaryar bata tsaya a nan ba, bayan wasu sa’o’i ta sake wallafa bidiyonta tare da kyakyawan angonta inda ta sha lalle tare da shigar amare suna daukar hotuna cike da soyayya. Jama’a sun taya ta murna.
Matar da ke da Tattaba Kunne 101 ta Bayyana Hotunan su
Ga wasu daga cikin tsokacin da jama’a suka dinga yi mata:
Jaruma Hadida Gabon dake amfani da @adizatou tace: “MashaAllah”
@dawayyarukayya85 tace: “InshaAllah, Ina taya ki murna.”
@realfatikk tace: “Allah ya sanya alheri.”
@teeskitchen1: “Na taya ki murna, Allah ya baku zaman lafiya.”
@meemaestee1: “Alhamdulillah, MashaAllah. Na taya ki murna, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya. Ameen.”
Fitacciyar jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta sanar da daina fitowa a fim.
A wani labari na daban, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Maryam AB yola, ta fitar da sanarwa a shafinta na Instagram inda tace daga ranar 1 ga watan Satumban 2020, ta bar masana’antar Kannywood.
Daga karshe ta mika godiyarta ga masoyanta, kawaye da abokan arziki a kan irin kaunar da ake gwada mata.
Kamar yadda ta wallafa a shafin nata: “Assalamu alaikum. Ni Maryam AB Yola ina mai sanar da ku cewa daga yau daya ga watan Satumban 2020, na daina yin fim kuma na bar Kannywood.
“Kuma ina matukar godiya da kaunar da kuke nuna min. Allah yasa mu dace, Ameen.”
Source:legithausang