A yau ma shafin Rumbun Nishadi na tafe da wani babban Jarumi wanda ya shafe kusan shekaru 20 a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wato Haruna Talle Mai Fata, inda ya yi wa masu karatu karin haske dangane da irin mummunan kallon da sauran al’umma ke yi wa masana’antar Kannywood tare da wadanda ke ciki a jimlace. Jarumin ya bayyana abubuwa masu yawan gaske dangane da abin da ya shafi fina-finan Hausa da kuma masana’ar gaba daya. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da dan takaitaccen tarihinka…
Assalamu akaikum warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu. Sunana Haruna Talle Mai Fata Sardaunan Samarin Arewa, kamar yadda ake kirana da shi a masana’antar Kannywood da sauran ‘yan kallo gaba daya. Ni dai an haife ni a Jos, iyayena kuma daga Kano gefen Babata wani bangaren daga Kano, wani gefen daga Katsina. Na yi makarantar firamare da Sakandare dina duk a Garin Jos, inda na tafi Bauchi na yi Jami’a, na tsaya a dai-dai deploma. Ina da mata da yara guda hudu, mata uku namiji daya, kuma a yanzu haka ina ci gaba da rayuwata a garin Jos.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Sana’ar fim sana’a ce wadda za ki ga mafi yawancin mutane idan suka ta so, musamman yara za ki ga sun taso da sha’awar son yin fim. To Gaskiya a gidanmu akwai wanda shi furodusa ne, kuma su ne suka fara yin ma fim a Jos, don in bai zo na biyu ba to zai zo na uku yayanmu ne, shi ya fara yi. Lokacin da ya fara yi sai ya dan kwadaita mun zai saka ni sai na kara jin sha’awar abin, to daga baya kuma ya zo Allah bai ba shi ikon saka ni ba, da ke gidanmu gida ne irin wanda duk wanda ya taso in har za ka iya magana ka iya tafiya, ka iya dagawa ka ajjiye a nan, komai kankantarsa tun da kin ga fata ba ta da nauyi, to kawai yana da sana’a duk sati za a biya shi, shi ne za ki ga kowa da dan kudinsa a hannunsa ko ba yawa, saboda gidanmu gidan kasuwa ne sana’ar babanmu muke, dukka fata muke saya da sayarwa, shi ne na ji kawai gara na yi nawa. A nan ne cikin ikon Allah na nemi wani Darakta da ya ke abokin shi yayan namu ne, Bello Muhammad Bello na bashi aiki ya yi min fim, nan take kuwa ya rubuta wani fim me suna ‘ZUCIYATA’, da ya rubuta ya kawo muka duba na ce ga rawar da zan yi a ciki, ni zan fito a jarumion fim din wato zan jagoranci fim din ya ce a’a! yanzu ya yi sauri ban taba yi ba na ce zan fito a jarumi in bari tukunna na nemi wani wurin a sa ni. Na nemi wasu jarumai a kannywood, da yake shi babban furodusa ne sai suka dan nuna mun na bari idan aikinsa ya zo sai su zo in sun yi masa sai su dan yi mun, kin ga zan samu sauki. To da na jira-na jira kawai sai na nemi shi daraktan na ce kai me ya sa ba za ka yi mun rol din ba?, ya ce zai iya mana shi Bello Muhammad Bello kenan, sai na ce ya yi mun mana, sai ya yi mun. Muka yi fim din cikin ikon Allah muka gama shi sa’annan kuma fim ya samu daukaka, sunan fim din ZUCIYATA, ni na fito a dan gwamna, daga wannan fim din gaskiya na fuskanci cewa zan iya, kuma abin ma da dadi saboda duk inda na je wucewa ana wane-wane, daga nan kawai sai na kara dauko wani ‘rubutun’ me suna ‘HAFSA Ko SAFIYA’ shi ma na yi, nan muka fito da wani jarumi Baba me sakata kenan, na manta ainahin sunan da ake fada masa, jaruminn sakata dai, shi ne nan ma muka je na yi wannan fim din, shi ma na fito irin kai da kai na yi kokari kamar ‘Boss’ da ‘Actor’ na fito rol me yawa fiye da na ‘ZUCIYATA’. Dana saki fim din sai na ga na samu alkhairi sosai, sai na gano cewa wannan fa sana’a ce da za ta rike mutum, Alhamdulillahi kuma gashi ta rike ni duk yawancin abin da na samu a rayuwata kaso casa’in ta wannan sana’ar ce.
Source: LEADERSHIPHAUSA