A ranar Asabar din nan ne, Maryam Shettima, wadda aka fi sani da Maryam Shetty, ta yi aure inda ta wallafa hotunan auren nata a shafukanta na sada zumunta.
Auren wanda ya zo da ba a zata, an daura shi ne ba tare da taron jama’a masu yawa ba.
Jaridar LEADERSHIP ta tuno da irin yadda Maryam Shetty ta rasa damar kasancewa mamba a majalisar ministocin shugaban kasa Bola Tinubu, wanda yanzu suke cika watanni goma kan kujerunsu.
A watan Agustan 2023, Tinubu ta zabi Shetty a matsayin wanda za a bawa minista daga Jihar Kano, sai da kuma daga baya Marayam Shetty ta rasa damar, bayan da aka canja sunanta da Dokta Mariya Bunkure.
Tun daga lokacin aka daina jin ɗuriyar Maryam Shetty, kwatsam! Sai labarin aurenta da ya karade kafafen sadarwa a wannan rana ta 8 ga watan Yuni, 2024.
Kafin dambarwar batun Minista Marya ta kasance shahararriya a kafafen sadarwa na zamani.
A wani labarin na daban ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Abuja, ya shirya bikin bankwana ga mahajjatan Nijeriya da za su halarci aikin Hajjin 2024.
Ambasada Faisal Ibrahim al-Ghamidy ne, ya jagoranci bikin wanda manyan jami’ai daban-daban, manyan baki, da kuma wasu mahajjatan da suka halarci taron.
Ambasada Al-Ghamidy ya jaddada kokarin da Saudiyya ke yi wajen samar da ingantacciyar hanyar don kyautata aikin Hajji.
Jakadan ya jinjina wa Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman bisa jajircewarsu na shawo kan kalubalen da mahajjata ke fuskanta.
Ya yi karin haske game da tsare-tsare da saka hannun jari da Saudiyya ta yi don tallafa wa miliyoyin musulmin da ke shiga kasar domin gudanar da aikin Hajji.
An kammala bikin tare da gabatar da kyaututtuka ga bakin Nijeriya, bakin sun jinjina wa masarautar Saudiyya kan irin kulawar da ta ke bai wa Nijeriya.
A wannan shekara, mahajjatan Nijeriya 30 ne, za su shiga cikin shirin baki na masu kula da masallatai biyu, wani shiri da aka tsara don bayar da kulawa da ayyuka na musamman ga mahajjata daga sassan duniya.
DUBA NAN: An Fara Kamo Maniyyatan Da Basu Da Shaidar Aikin Hajji A Saudiyya
Shirin wani tsari ne mai daraja wanda a kowace shekara yake daukar nauyin mahajjata daga kasashe daban-daban, wanda zai ba su damar gudanar da aikin Hajji tare da taimako daga Masarautar Saudiyya don taimaka wa al’ummar musulmin duniya.