Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar APC, Sanata Kashim Shettima, yace idan suka ci zaɓen 2023, gwamnatin Bola Tinubu, zata kawo karshen matsalar tsaro cikin watanni shida zuwa shekara ɗaya.
Shettima ya faɗi haka ne a wurin taron Bola Tinubu da ‘yan kasuwa ajihar Legas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“A tsakanin watanni Shida da shekara ɗaya, shugaba na (Bola Tinubu) zai haɗa tawagar da zata kawo ƙarshen wannan rashin hankalin,” inji shi.
Ku dakaci karin bayani…
A wani labarin na daban kuma hankulan masoya mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da ‘Davido’ sun tashi yayinda jita-jitan mutuwar dan masoyiyar sa, Chioma Rowland, ya bazu.
Rahotanni sun bayyana cewa yaron ya mutu ne cikin rafin wanka na shakatawa dake cikin gidansa dake unguwar Banana Island dake jihar Legas.
An fito da yaron dan shekara 3 daga cikin ruwan kuma aka garzaya da shi asibiti inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming Pool.
Source:legithausang