Abubakar Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, zai cika shekaru 60 a gobe Litinin.
Saraki ya tafi kasar Saudiyya domin yin Umara tare da godiya da wannan ni’ima da Allah ya yi masa.
Masoya sun taya dan siyasar murna da fatan alkhairi, inda wasu da dama suka ce suna kewarsa a majalisa.
A ranar Litinin, 19 ga watan Disamba ne tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki zai cika shekaru 60 a duniya.
Domin raya wannan rana, Saraki ya garzaya kasa mai tsarki don nuna godiya ga Allah madaukakin sarki.
“Nan da ‘yan awanni zan cika shekara 60 a duniya, bisa haka ne na zo birnin Madinah domin yin godiya ga Allah.”
Ko ba komi, yayin da Allah ya tambaye mu a littafinsa mai tsarki, cikin Surah Ar-Rahman da cewa; “Wanne daga ni’imomin Mahaliccinku ku ke ƙaryatawa?
Amsarmu ita ce, BABU!” Jama’a sun yi martani Yusuf Bayero ya yi martani: ”
Allah ya karba shugaban majalisar dattawa da ya fi kowanne a tarihi Najeriya ina yi maka fatan samun tsawon rayuwa, wadata da kariyar Ubangiji.”
Nazir Kabir Hali ya ce: “Allahu Akba Lallai Sir Kayi Tunani KumaAllah Ysm Sauran Rayuwarka Albarka Ys Ka Cira Duniya Da Lahira Don Annabi Da Al-Qur’ani.”
Abdurrahman Mukhtar Tody ya ce: Masha Allah. Allah qaro masu Albarka, Gaskiya muma Allah ubangiji ya Mana Arziqi.”
Suleman Umar Hussain ya ce: “Allah ya kara shekaru masu albarka, mun yi kewar shugabancinka a majalisar dattawa, yanzu muka san muhimmancin rashinka, Allah ya karo albarka yallabai.”
Garba Mustapha ya ce: “Masha ALLAH Najeriya na kewarka a matsayin shugaban majalisar dattawa saraki.”
Muntari Rabi’u Bichi ya yi martani: “Masha Allah. Alhamdulillah. Allah ya Karo Ma Su Albarka.”
A wani labarin, a ranar Asabar, 17 ga watan Disamba ne shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya cika shekaru 80 a duniya.
Domin raya wannan rana, hadimin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na aPC, Joe Ibokwe ya yi shagube ga abokan adawar Buhari.
Ya ce duk da rade-radin ake ta yi cewa ya mutu, yau ga shi Allah ya raya shi har ya kai shekaru 80 a duniya.