Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama MK, wadda aka fi sani da Hajiya Rabi Bawa Mai Kada a cikin shiri mai dogon zango na kwana casa’in ta haifi santatleleiyar jaririya a gidan Aurenta na gaskiya.
Rahama ta yi shura a fina finan Hausa musamman shiri mai dogon zango na kwana casa’in da gidan talabijin na Arewa 24 ke haskawa.
Jaruma Mansura Isah ce ta bayyana batun haihuwar a kafar sada zumunta ta Instagram inda take taya Rahama murnar samun karuwar diya mace a zahiri.
A wani labarin daban daya daga cikin fitattun Jaruman fina-finan Hausa cikin masana’antar Kannywood, kuma Jarumi mai taka rawa a cikin shirin Dadin Kowa na Arewa24, wanda ya shafe shekaru sha biyar a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, MUHAMMADU MURTALA wanda aka fi sani da DANTANI MAI SHAYI. Ya warware zare da abawa game da abubuwan da masana’antar ke bukata a wajen duk wani me shirin zama jarumi. Bugu da kari jarumin ya yi kira ga gwamnati game da irin matsalolin da masana’antar ke fuskanta tare da hanyar magance su. Dadin dadawa jarumin ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta yayin shiga cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi rayuwarsa. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ka fadawa masu karatu cikakken sunanka tare da dan takaitaccen tarihinka?
Sunana Muhammadu Murtala wanda aka fi sani da Dan Tani Mai Shayi a Dadin Kowa. An haife ni a unguwar ‘Brigade’ Kabarin Rakka, na yi firamare a ‘Kawo Unguwar Gaya Special Primary School’ da ke Unguwar Gaya. Daga nan na tafi ‘Secondary School Stadium’, daga nan kuma na je KAS. Ina da mata guda daya da yarinya daya.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood?
Abin da ya ja hankalina har na shigo cikin masana’antar shi ne, Tun a makarantar Sakandare irin dirama irin wadda ake yi a makaranta, shi ya ja hankalina. Daga nan sai muka kafa kungiya ta dirama mai suna ‘Kainuwa’, mun kafa ta a Badawa, daga nan kuma sai muka yi wata kungiyar a Dakata, sai kuma muka yi Le Jan Zaki, daga nan sai na dawo nake Sakatare na Ali Jita, tun lokacin muke tare da Ali Jita har kawo iyanzu. Bayan nan kuma na tafi Arewa24 muke Dadin Kowa, amma ban da Dadin Kowa na yi fina-finai da yawa, kamar su; Sabuwar Sangaya, Sarkin Barayi, da dai sauransu suna da yawa.
Gaskiya akwai gwagwarmaya sosai, ka tashi ka shiga nan, kai ne can. Ita harkar industiri daman farko kar ka sa ran sai ka samu kudi a cikinta, farko ka fara da neman suna shi ne farko, kuma sai ka zamto mai ladabi da biyayya, sai ka zamto mutum ne me sirri, sai ka zamto mutum ne mara rainuwa, sai ka zamto mutum ne mara daukar magana ka kai nan – ka kai can. To indai kana haka to za ka ci gaba kuma ka zamto mai addu’a, kuma ka rike iyayen gida masu amana, wannan ita ce kadan daga cikin gwagwarmayar Industiri, ka ji – ka ki ji, ka gani – ka ki gani, haka harkar take.
Source LEADERSHIPHAUSA