Shahararriyar mai amfani da kafar sadarwa ta TikTok Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewar a duk lokacin da ta tuna cewar akwai kwanciyar kabari sai hankalinta ya tashi.
Murja ta bayyana haka a wani dan gajeren bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok a yau Laraba.
Ta kara da cewar daga cikin abubuwan da suke tayar mata da hankali idan ta tuna akwai kwanciyar kabari.
“Idan na tuna cewar bayan na mutu dole ne za a sanya ni a cikin kabari daga nan sai hankalina ya yi matukar tashi” cewar Murja.
A wani labarin na daban tsohuwar jaruma a masana’antar Kannywood, Hajiya Fati Ladan, ta bayyana dalilin da ya sa take har yanzu a gidan mijinta duk da cewar ana cewa ‘yan fim ba su cika zaman aure ba, kuma ta yi fatan Allah ya kashe ta a dakin mijinta.
Fati ta yi wadannan kalaman ne a hirar da ta yi da manema labarai dangane da cikar ta shekara goma cur a gidan aure a gidan mijin ta a Kaduna.
Fati da Yerima dai su na da ‘ya’ya biyu a tsakanin su, A’isha Humaira da Muhammad Shafi’u, kuma su na zaune ne a Kaduna. Fati ita ce amarya a cikin matan sa biyu.
Da take amsa tambayoyin yan jarida Fati ta bayyana matukar godiyarta ga Allah (S.W.T.) da ya nuna mata wannan lokaci inda ta bayyana shekara goma ba kwana goma ba ne.
Ta kara da cewar zaman aurenta na tsawon shekaru 10 ba wani sirri ba ne illa kawai hakuri da soyayya saboda soyayya idan babu hakuri, sai ka ga kuma ba za a kai ga cimma inda ake so a kai ba.
Saboda a duk lokacin da mutum ya ce zai yi abu, musamman aure, to ina tunanin ba wasa ya je yi ba, aure abu ne wanda in har ka yanke hukuncin cewa za ka yi shi, ka san da sanin cewa ibada za ka je ka yi ba sharholiya ba.
A lokacin da na yanke shawarar zan je in yi aure, na sanya wa zuciya ta cewa zan je in zauna, ibada zan yi wannan abin da na sa wa rayuwa ta ya sa ban fuskanci wani kalubale dangane da zaman aure na ba ko in ji ina kewar wani abu ba.
Kuma miji na ya na ba ni goyon baya dari bisa dari a dukkan abin da na ce zan yi in dai bai saba wa addini na ba da al’ada ta zai ba ni goyon baya.
Hakan ne ya sa na maida shi kamar aboki a wuri na, shi kuma ya maida ni kawa a wurin shi duk abin da za mu yi, mu na yin shi tare da ni da shi ban yi ‘missing’ din wani abu ba, gaskiya, saboda duk abin da na ke nema ina
samu a wurin miji na.
Source: LEADERSHIPHAUSA