Bayan yan kwanaki tsare a gidan yari, an sake gurfanar da Murja Kunya gaban kotu a jihar Kano.
Hukumar yan sanda ta damke Murja ne yayinda take shirin bikin ranar haihuwarta a jihar Kano.
Alkalin kotun a karo na biyu bai bada belinta ba, ya ce a cigaba da tsareta a gidan gyara hali.
A yau Alhamis, 16 ga watan Febrairu, shahrarriyar yar dandalin TikTok, Muurja Ibrahim Kunya, ta sake gurfana gaban kotun shari’ar Musulunci dake Filin Hoki jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya.
Arewa Radio ta ruwaito cewa Alkali Mai Shari’a yayi umarni a maida Murjaa Ibrahim Kunya gidan gyaran hali da tarbiyar zuwa mako guda.
Murjaa dai har ila yau ta musanta tuhumar da ake yi mata a gaban kotu.
Freedom Radio ta ruwaito cewa game da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba.
Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba. Damke Murja Ibrahim Kunya.
A farkon watan nan, an gurfanar da shahrarriyar Ƴar TikTok ɗin nan Murjaa Ibrahim Kunya gaban Kotun shari’ar Muslunci dake Filin Hoki a jihar Kano.
Ta gurfana ne ranar Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023. Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.
An karanto mata tuhumar da ake mata inda nan take ta musanta, daga nan ne kuma lauyanta, Barrister Yasir Musa, ya nemi a bada belinta.
Alkali mai Shari’a Abdullahi Halliru ya yi watsi da wannan bukata na lauyan Murja Ibrahim Kunya kuma ya bada umurnin jefa ta gidan ajiya da gyaran hali.
Lauyan Murja ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari amma Alkalin kotun ya sake watsa masa kasa a ido.
Source:LegitHausa