Wasu da ba a san ko suwaye ba sun yi wa fitacciyar matashiya ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya dukan tsiya a yammacin yau a Kano.
A hotunan matashiyar da suka bayyana a shafukan sada zumunta da har Leadership Hausa ta samu gani bata-garin sun canza mata kama da raunuka a fuskarta.
Tuni dai aka fara yin kira ga jami’an tsaro da su bi mata hakkinta ta hanyar zakulo wadanda suka yi mata wannan aika-aika.
Murja Ibrahim Kunya dai tayi kaurin suna a shafin TikTok inda take da mabiya masu dimbin yawa,dake bibiyar shafin nata.
Kuma yar gwagwarmayar siyasa ce da take goyon bayan Gwamnan jahar Kano Eng Abba Kabir Yusuf.
A wani labarin na daban kungiyar Kwadago ta Nijeriya NLC, ta ce babu wata yarjejeniya tsakaninta da gwamnatin tarayya na janye yajin aikin da ta shirya yi a ranar 3 ga watan Oktoba.
Mista Benson Upah, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.
Idan dai ba a manta ba a karshen taron majalisar zartaswar kungiyar kwadago ta kasa NLC da TUC sun shelanta yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata don janyo hankalin gwamnati ta amsa bukatunsu.
Upah yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da ake zargin Mista Olajide Oshundun, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka ya fitar.
Upah ya ce akwai wasu sabani a cikin sanarwar da suka hada da yajin aikin da ake shirin yi da kuma mamaye sakatariyar kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) ba bisa ka’ida ba.
“Saboda haka, mun ga ya zama dole mu yi karin haske. Na farko dai ba mu da wata yarjejeniya da gwamnati na dakatar da shirin yajin aikin.
“Ba mu da wata rana da za mu gana da gwamnati da za ta kai ga dakatar da yajin aikin da ake shirin yi.
“Duk da cewa ba mu da niyyar wulakanta ofishin mai girma Ministan Kwadago da Aiki, wannan lamari ya wuce ma’aikatar.
Ya kara da cewa “Ya kamata wannan ya fito fili a gare su yayin ganawarmu ta baya-bayan nan.”
Don haka ya yaba da rawar da Ministan Kwadago da samar da Aiki, Mista Simon Lalong ya taka wajen ganin an sako shugabannin NURTW daga tsaren ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba.
Source LEADERSHIPHAUSA