Wani matsahi ya bayyana rashin jin dadi da ya fuskanta bayan ya gayyaci wata budurwa zuwa gidansa ta kwana.
Wannan matsahi ya bayyana cewa ya gayyace ta gidansa kuma ya kyalle ta ta kwana sannan ta kama hanya ta tafi da safe Amma, a tsakar dare, matar ta yi barci mai nauyi sannan ta fara munshari hakan ya bata masa rai.
Wani mutum dan Najeriya ya bayyana abin da ya faru tsakaninsa da wata yarinya da ya gayyata zuwa gidansa ta kwana.
Ya bayyana cewa sun kwanta tare kuma ya yarda ta yi barci a gidansa sai ta tafi da safe. Matashi ya gayyaci budurwa gidansa.
Amma a tsakiyar dare, matashin ya kasa yin barci saboda yarinyar tana munshari mai zurfi yayin da suke kwance.
Da ya ke wallafa bidiyon a TikTok, mutumin cikin bacin rai ya roki masu bin sa a dandalin sada zumuntar su tallafa masa.
Abin da masu amfani da dandalin sada zumunta suka ce game da bidiyon @h.afsattt ta ce: “Karar tamkar janareta.”
@irawo4real ya yi tsokaci: “Ka wahal da ita sosai ne.”
@simbioyedele cewa ya yi: “Da na fada wa yarinyar an kira ni a wurin aiki kuma babu wanda zai taya ni.”