Wani matashi dan shekara 19 ya dirka wa malamar sa mai shekaru 28 ciki, inda malamar take rokon shi ya taimaka ya aure ta.
A lokacin da wannan matashi ya sanar wa mahaifin shi, Richard Nana Sam, cewa yayi da gangan ya zabi mace ta koyar da dan shi saboda bayaso namiji A lokacin da wannan matashi ya sanar wa mahaifin shi, Richard Nana Sam, cewa yayi da gangan ya zabi mace ta koyar da dan shi saboda bayaso namiji yazo ya dirka wa diyar sa ciki.
Bayan Richard ya wallafa labarin, mutane da dama sun hanzarta zuwa sashin tsokaci, don bashi mafita game da matakin da ya kamata ya dauka.
Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.
Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar ‘yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe.
Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki, za ta haife shi.
Richard ya bayyana yadda yayi wa yaran shi tagwaye (namiji da mace) masu shekaru 19 hayar malamar da za ta dunga koya musu karatu a gida.
Malamar ta ce, tana dauke da ciki wata uku Kamar yadda Richard ya fadi, ya tabbatar da bai zabi malami namiji ba, saboda ba zai iya kasadar dawowa gida wata rana yaji labari mara dadi tsakanin mai koya karatun da diyarsa ba.
Amma ga mamakin sa, malamar mai shekaru 28 tazo wurin shi wata rana, ta na shaida mishi labarin abunda yayi kokarin guje mawa.
“Masoya na, bayan wata takwas da ta dauka tana koyar da yara na, wata rana malamar ta zo ta shaida mun tana dauke da cikin yaro na wata uku, inda shi yaron nawa ya amince da lallai cikin nashi ne.
“Ta ce, ta na kaunar yaro na, saboda haka tana so in yarje musu su yi aure,” a cewar Richard.
Martanin jama’a Tsokacin yan soshiyal midiya: “Theodora Mawuse Norvor cewa yayi:”Wani lokaci mika lamarin yaran kake ga Ubangijin da ya baka su.
A matsayin ka na dan adam, duk iya son da kake wa yaron ka, kuma ka ke son kare su, ba za ka iya ba, Ubangiji kawai zai iya.”
Nana Ama Darkowaa ya nuna: “Mafitar a nan shi ne amincewa da cikin, kula da bukatun matar har ta haihu.
Sannan ka gamsar da yaron ka cewa, ba zai iya aure a shekarun shi ba, a halin yanzu dole ya maida hankali a kan karatun shi, sai yayi aure daga baya idan ya mallaki hankalin kan shi, koda da malamar shi ce.”
Kabeiku Quansah ya bayyana cewa: “Ina rokon ka da kada ka bari su yi aure fa!
Waye ya ce soyayya ne kadai matakin aure. Ka bar yaron ka ya cigaba da neman ilimin shi, alabashshi ka cigaba da kula da cikin, tunda ya amince da nashi ne.”
A wani labari na daban, sannanen abu ne cewa a makon da ya gabata masana’antar Kannywood ta rincabe tare da rikicewa da hargitsi tun bayan batun Ladin Cima da kuma bidiyon Naziru Sarkin waka inda ya zargi cewa ana lalata da ‘yan matan masana’antar kafin a saka su a fim.
A daren jiyar Lahadi ne jaruma Nafisa Abdullahi ta saki takarda inda ta yi wa Sarkin wakan martani kan ikirarinsa.