Aji Bukar Hazuki matashi ‘dan Najeriya ne mai shekaru 15 dake zama a Maiduguri, babban birnin jihar Borno wanda ya kayatar da ‘yan Najeriya da hazakarsa.
Matashin yaron ya kirkira tare da kera karamin Masallacin Makka wanda yayi sak da na Saudiyya kuma hotunan sun bazu tare da birge jama’a.
Wannan fasaha ce da ba kowa ke da irin ta ba saboda jama’a da dama sun dinga yabawa matashin yaron wanda suka ce zai dace da fannin kere-kere.
Hotunan babban masallacin Makka da matashin yaro ‘dan asalin Maiduguri ya kera ya matukar kayatar da jama’a.
Matashi mai shekaru 15 a duniya ‘dan asalin Maiduguri ta jihar Borno mai suna Aji Bukar Hazuki ya birge jama’a masu yawa a soshiyal midiya.
Leadership ta wallafa hotunan fasahar yaron a shafinta na Twitter inda tace lamarin ya faru a jihar Borno.
Jama’a sun bayyana yadda ya matukar birge su ganin cewa yaron bai bari hazakarsa ta dishe ba duk da shekarun da aka dauka babu zaman lafiya a yankinsu.
Borno tana daya daga cikin manyan jihohin da ta’addancin Boko Haram suka yi katutu na kusan shekaru goma.
Dubban jama’a sun rasa rayukansu yayin da ‘yan ta’addan suka mayar da mutane masu yawa zuwa ‘yan gudun hijira. Gidaje da iyalai duk sun rushe tare da tarwatsewa.
Bayan tsananta yaki da ta’addanci a fadin jihar, dukkan inda ‘yan ta’addan suka kafa tutocinsu an kwace sakamakon kokarin dakarun sojin Najeriya, lamarin da yasa kungiyar ta koma kai farmaki kauyukan Borno.
Jama’a sun yi martani Amacool Chibuike ya bayyana mamaki da inda yace: “Kai, gaskiya wannan abu ya birge.” @cloudmanteam yace:
“A gaskiya wannan abu ya kayatar.”
Ba wannan bane karo na farko da ‘yan Najeriya ke nuna hazakarsu a kira ba Tabbas ba wannan bane lokaci na farko da aka fara ganin ‘yan Najeriya masu kananan shekaru suna bayyana hazakarsa da Allah ya basu ba a fannin kirkire-kirkire da fasaha ba.
Wani matashi a kwanakin nan ya sanyawa wa babur dinsa sitiyari inda yake tuka shi tamkar mota a jihar Delta.
Source:Legithausa