Wani bidiyon da tsohon mawaki Kelly Handsome ya fitar ya ja hankalin mutane masu tarin yawa bayan ya nuna lokacin da wata budurwa ta kusa ba wa saurayinta guba amma manajan Otal ya fallasa ta.
Bidiyon ya nuna lokacin da manajan otal din ya fito daga ofishinsa a gaggauce domin ya hana jarumin fim din shan lemun da aka zubawa guba.
Mawaki Kelly Handsome a martaninsa kan bidiyon, ya ja kunnen maza da su kiyayewa wasu matan da suke soyayya dasu don halayensu babu mai kyau.
Wani bidiyon manajan otal da ya ceci jarumin fim din kudancin Najeriya yayin da budurwarsa ta zuba masa guba, ya bayyana a shafin tsohon mawaki Kelly Handsome kuma ya janyo maganganu daban-daban.
Jarumin da ya matukar shan mamaki kan mugun nufin budurwar, ya kusa zaucewa bayan an nuna masa bidiyon da CCTV ta nada wanda manajan otal ya gani ana kokarin halaka shi.
Da gaggawa manajan otal ya fito ya hana shi shan lemo Manajan otal din ya hanzarta fitowa daga ofishinsa inda ya dakatar da jarumin daga kwankwadar lemunsa.
Har yanzu dai ba a tabbatar da sunan jarumin masana’antar fim din kudun a yayin wallafar nan.
Hakazalika, bidiyon ya janyo martanin jama’a daban-daban inda wasu ke tambayarsa abinda yayi wa budurwar har take kokarin halaka shi.
Martanin jama’a Mutane da yawa sun yi caa kan bidiyon inda mamaki ya kama su.
Ga wasu daga cikin martanin jama’a: @xplicithayourella yace: “Kuma har tana da bakin magana.”
@bisiolumide: “Ina so in yarda cewa wannan bidiyon barkwanci ne.
Ta yaya wani zai yi kokarin halaka wani kamar haka.”
@de_yorubaghai_mfrn yace: “Karfin halin yayi yawa kuma har wasu ke ce mishi ya kwantar da hankalinsa?”
@skinglow_withfruitsandherbs: “Don Allah an kai ta kotu? Ya dace a ce tana gidan kurkuku a yanzu saboda Allah kadai ya san yawan wadanda ta halaka da wannan muguntar ta.”
@funnyboneofficial: “Martaninsa ne ya sage min guiwa, shiri ne gaskiya.”
@kess_duke_: “Wannan mutumin yayi godiya ga hukumar otal din da suka mallaka CCTV. Idan da wasu otal ne wannan gayen da yanzu ya zama gayu.”
@dsquare_boutique: “Sihirin soyayya take son zuba masa, amma ba zai yuwu ta zuba masa guba a fili haka ba.” Manajan Otal Ya Fallasa Budurwa da ta Zubawa Saurayi Guba a Lemo.
Source:LEGITHAUSA