Wani dan magidanci Najeriya mazaunin kasar Jamus mai sun Ebele ya koka a soshiyal midiya kan rikicin da ya dabaibaye auren sa.
Mutumin ya koka cewa matar da ya aura a Najeriya sannan ya kaita Turai ta zame masa karfen kafa.
Yayin da yake bidiyon matar ba tare da saninta ba, Ebele ya zarge ta da kwanan waje da bin maza.
Ebele, wani dan Najeriya mazaunin kasar Jamus, ya nemi taimakon masu amfani da soshiyal midiya kan mugayen halayen matarsa.
A wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, magidanci ya ce ya rasa sukuni tun bayan aurensu da matar.
Ebele ya ce ya je Najeriya, ya auri matar sannan ya kawo ta Jamus inda yake zama amma ta zama abun da ta zama.
Ya ce: “Ban cancanci wannan ba dukka…
Matar da naje Najeriya na auro ta da kudina…”
Ya zargeta da keta haddin aure sannan ya dauki bidiyon zazzafan muhawarar da suka yi ba tare da saninta ba.
A bidiyon, matar ta karyata shi. Ta ce ta dawo daga wani bikin zagayowar ranar haihuwa a daren jiya kawai sai ta tarar da fusataccen mijin nata a haka.
Sai dai mijin ya nace cewa namiji ta bi ba biki ba
Jama’a sun yi martani Uluma Esther ya ce: “Irin wannan matar sune suke batawa salihai suna, idan ka auri salihar mace za ka ji tsoron tafiya da ita can zata chanja, Allah ka taimake mu, kada ka bari bata gari su bata mana harkoki.”
Adesewa Y Adedayo ta ce: “Kafin najimi ya iya fitowa fili ya koka haka ka san cewa matar ta tunzura shi matuka. Idan matar aure na ganin wani namijin a lokacin ne za ka ga tana bayar da uzuri iri-iri.”
Ruth Emmanuel Omonyemhen ta ce: “Na san irin radadin da kake ji duk da cewar ni mace ce, amma ka sani karen da ke raye ya fi mataccen damisa, Allah ya share maka hawayenka.”
Matar aure ta roki budurwar mijinta ta dawo gare shi ko ta samu nutsuwa
A wani labarin, wata matar aure ta garzaya shafin soshiyal midiya inda ta yi bidiyo hade da rokon budurwar mijinta ta dawo gare shi ko ta samu ta sarara a gidan auren ta.