A wani bidiyo da shafin kafar watsa labarai ta TRT Hausa ta wallafa a shafinta na Tuwita an ga yadda wata mage ta daka tsalle ta fado kan Liman yayin da yake jan jama’a Sallah.
Lamarin ya faru ne a Masallacin Abubakar al Siddiq da ke wani birni mai suna Bordj Bou Arreridj da ke kasar Algeria kamar yadda kafar TRT ta rawaito.
Ko kadan limamin Masallacin bai razana ko tsorata ba yayin da magen ta fado masa babu zato babu tsammani.
Mage (mace) ko kuma Muzuru (namiji) na daga cikin dabbobin da mutane da yawa suka aminta dasu har suke ajiyewa a gidajensu domin debe musu kewa.
Sai dai, duk da haka har yanzu akwai wasu mutane dake matukar tsoron mage, wasu ko gidan da ake kiwon mage basa iya ziyarta saboda tsananin tsoron mage.
Koda mutum baya jin tsoron dabbobin da ake ajiyewa a gida, a mafi yawan lokuta mutum kan razana tare da firgita idan irin wadannan dabbobi suka fado kansa ko kuma suka yi motsi ko kuka babu zato babu tsammani.
Sabanin irin wadannan mutane dake razana ko firgita idan dabbobin da suke kiwo sun fado kansu ko sun yi kuka babu tsammani, Limamin Masallacin Abubakr al Siddiq da ke birnin Bordj Bou Arreridj da ke kasar Algeria ya bawa mutane mamaki saboda jarumtarsa.
Ko gezau limamin bai yi ba a yayin da wata mage ta daka tsalle ta fado kansa a yayin da yake cikin rera kira’ar Alqur’ani mai girma a lokacin da yake jan jama’a sallah.
A faifan bidiyon da shafin watsa labarai na TRT da ke kasar Turkiyya ta wallafa a shafinta na Tuwita (@trtafrikaHA) za’a iya ganin yadda magen ta yi tsalle ta haye kan kafadar Malam Liman kafin daga bisani ta hau tsakiyar kansa tare da gangarowa zuwa kan kirjin sa.