Tsaunin Kilimanjaro da ke Tanzania ne tsauni mai tsayi a Afirka inda ake hasashen tsayin nasa ya kai mita 5,895.
Ana bayyana shi a matsayin tsauni mafi girma da ke tsye shi kadai a duniya. Wannan na nufin ba wani bangare na wani tsaunin ba ne. SHi kadai yake tsaye.
Tsaunin na da kololuwa uku da ke tarihin aman wuta; Kibo da Mawenzi da Shira. KIbo ne mafi tsayi kuma a nan ne wajen da ya fi tsini a kan tsaunin da ake kira Uhuru yake.
Duk da ksancewar sa a Tanzania, ana iya ganin wannan tsauni a kurkusa a Kenya da ke makotaaka.
Masu yawon bude ido na kallon Kilimanjaro daga Babban Filayen Shakatawa na Kasa na Kenya da suka hada da Filin Amboseli, da Tsavo West.
Saboda wannan, kamfanunnukan yawon bude ido a Kenya suke sanya kudade don zagayawa da ‘yan yawon bude ido kewayen Kilimanjaro.
A 1987, UNESCO ta saka Tsaunin Kilimanjaro a Jerin Kayan Tarihi na Duniya saboda kyawun da wajen ke da shi. Hawa Tsaunin Kilimanjaro na bukatar shiri sosai na zahiri da baɗini.
Akwai hanyoyi bakwai da aka amince a hukumance da a yi amfani da su wajen hawa Tsaunin,, kuma ana daukar kwanaki daga biyar zuwa goma don kai wa ƙololuwarsa.
Kamfanonin yawon buɗe ido na cajin daga dala 2,000 zuwa dala 3,000 don yin tafiyar.
A kowacce shekara mutane dubu 30,000 zuwa 50,000 ne ke ziyartar Tsaunin Kilimanjaro, kamar yadda gwamnatin Tanzania ta bayyana.
Dan yawon bude ido na kuma bukatar biyan dan jagora a kalla dala 20 da dala 25 a kowacce rana, mataimakin dan jagora kuma dala 15 da dala 20, inda ake biyan mai dafa abinci dala 15 a kowacce rana.
Dadin ga masu yin hidima a yayin hawa tsaunin, akwai kuma ma’aikata irin na otel, kamfanonin shirya tafiye-tafiye, kamfanonin jiragen sama da ke samun kudade albarkacin wannan tsauni.
Lokacin da ya fi dacewa da hawa Tsaunin Kilimanjaro shi ne tsakanin watannin Disamba da Maris ko daga watan Yuni zuwa Oktoba.
Wadannan lokuta ne da ba a samun ruwan sama sosai, hanyoyi suna zama bushe.
Ana fara tafiyar a dajin emerald, wand ayana dauke da dabbobin dawa da dama. Sannan sa a bulla wani waje mai busasshiyar kasa kuma kewaye da furenni nau’i daban-daban.
Sannan sai ku isa ga dajin kan tsauni da ke yin iso ga sararin da ke da kankara. A nan za ku isa ga kololuwar Afirka!
DUBA NAN: Ana Rantsar Da Shugaban Kasa Mafi Karancin Shekaru A Senegal
Gwamnatin Tanzania ta bayyana cewa a kowacce shekara mutane dubu 30,000 zuwa 50,000 ne ke ziyartar Tsaunin Kilimanjaro. A kowanne lokaci ana samun a kalla mutane 1500 a kan tsaunin