Garken giwayen Asiya wadanda kaurarsu ta dauki hankalin kasa da kasa, sun shiga garin Shijie dake birnin Yuxi, a lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Wani toron giwa, wanda ya fice daga cikin garken giwayen kwanaki 9 da suka gabata, yanzu haka ya yi nisan kusan kilomita 17.4 daga dangin sa, kuma dukkanin giwayen 15 suna cikin koshin lafiya da tsaro, kamar yadda hedkwatar dake sa lura kan kaurar giwayen ta bayyana.
Kimanin wata guda ke nan, hukumomin kasar Sin suka tura jami’an ’yan sanda domin yiwa garken giwaye din rakiya, tare da share musu hanyoyin mota don su samu damar wucewa, kana jami’an na ajiye abinci domin dauke hankalin giwayen don kaucewa shiga yankunan dake da cunkoson jama’a.
Tawagar giwaye da suka baro dajin Xishuangbanna Dai zuwa Kunming, a yanzu sun fara kewaye a garin Shijie dake birnin Yuxi na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Nau’in Giwaye na Asiya suna karkashin kulawar kasar Sin a mataki na A, inda galibi ake samunsu a lardin Yunnan. Bisa namijin kokarin da ake yi wajen ba su kariya, a yanzu haka, adadin giwayen dajin sun karu zuwa kusan 300, daga adadin 193 a shekarun 1980.
Namun daji na zaman wata babbar hanyar bude idanu da kuma samun kudin shiga ga gwamanatocin kasashen kuma namun daji irin su giwa, damisa, zaki da dai sauran su sukan samu kulawa gami da samun kariya ta musamman daga hukumomi sakamakon barazanar karewar wasu irin dangin na namun daji da yake faruwa wanda hakan ke zaman babbar barazana ga wanzuwar lamarin namun daji a duniya baki daya.