Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada darakta Ishaq Sidi Ishaq matsayin mai bashi shawara na musamman.
Kamar yadda darakta Falalu Dorayi ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya taya Ishaq murna inda yace sai ya dage.
Gwamnan ya nada tsohon jarumin kuma darakta a matsayin mai bashi shawara na musamman a fannin kirkira Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nada daraktan fina-finai, Ishaq Sidi Ishaq mai bashi shawara na musamman.
Kamar yadda takardar nadin ta nuna, Ganduje ya nada Ishaq ne matsayin babban mai masa hidima ta harkokin kirkira wato Creative Industry. S
anannen daraktan fina-finai, Falalu Dorayi ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi inda yake cewa: “Muna taya darakta Ishaq Sidi Ishaq murnar samun mukamin babban mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a fannin kirkira.
“Tabbas akwai kalubale amma sai kayi da gaske. Domin tukunyar sama ce ragamarta ta dawo hannunka. Allah ya baka ikon aiki da adalci.”
A da dai Ishaq Sidi Ishaq jarumi ne a masana’antar Kannywood daga bisani kuma yafi karkata ga fannin bada umarni.
Tabbas ya dade ana damawa da shi a masana’antar fina-finan hausan duk da a cikin kwanakin nan ba a jin duriyarsa.
A wani labari na daban, matasa a yankin Itapgbolu dake karamar hukumar Akure ta arewa dake jihar Ondo sun fatattaki basaraken yankin bayan mutuwar wani dan sanda mai suna Ayo Oloyede. Oloyede dan sanda ne dake aiki da sashen yaki da kungiyoyin asiri dake karkashin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo kafin mutuwarsa a ranar Lahadi da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.
Ganau ba jiyau ba sun sanar da yadda matasa a yankin suka taru sannan suka kori basarake, Oba Idowu Faborade, Ogbolu na Itaogbolu daga fadarsa bayan labarin mutuwar Ayodele ya karade gari. An tattaro cewa, marigayi Oloyede ya ziyarci mahaifiyarsa kuma yana komawa Akure ne lokacin da motar hayan da yake ciki ta kifa tare da tintsirawa tsakanin Itaogbolu da kauyen Odudu.