Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa, shine da kansa ya shiga ya fita har sabon shugaban hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu ya samu wannan mukami.
Rarara ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida, inda ya kara da cewa, yayi matukwar farin ciki da Ali Nuhu ya samu wannan mukami.
Da yake amsa tambayoyin yan jarida akan ko gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu wadda yayi ikirarin kafawa ta biyashi aikin da yayi mata a lokacin yakin neman zabe ta hanyar nada amininsa kuma jarumi Ali Nuhu matsayin shugaban hukumar Fina Finai ta Nijeriya?
Rarara ya amsa da cewa, “ko kusa wannan abu da aka yi wa Ali Nuhu ba shine zai nuna an biya ni aikin da na yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba, duk da cewa naji dadi sosai akan wannan mukami da Ali Nuhu ya samu amma wannan bai zama dalilin da zai sa ace an biyani ba.”
A wani labarin na daban shahararriyar ‘yar wasan fina finan Hausa ta Kannywood Aisha Humaira kuma ta kusa da mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara.
Ta bayyana cewar babu bukatar a dinga zagin Rarara don kawai ya yi wakar kidaya kuma ya sanya gasa a kan wakarsa.
Aisha Humaira yayin wani gajeren bidiyo da ta dora a shafinta na Tik Tok ta ce don Rarara ya saka gasa akan wakarsa ta Kidaya ba shine zai nuna cewar baya kishin Arewa ba.
Domin ai ya taba yin waka inda ya fadi matsalar rashin tsaro da jaharsa ke fama da ita, kuma a wancan lokacin wakar ta karbu.
Mafi yawancinmu yan Arewa mune matsalar yankinmu domin ba mu da wani aiki sai idan mutum ya kawo wani abu sa mu bi duk wasu hanyoyi mu ga cewar mun kassara wannan abin.
Wasu na cewa wai kwangilar wakar kidaya aka bai wa Rarara,to idan ma haka ne ai ya taimaka domin a cikin kudin kwangilar ne yake son duk wanda ya samu nasara a gasar kidaya a bashi dan wani abu shima.
Kuma matsalar tsaro babu abin da banganiba domin ni ‘yar Maiduguri ce jihar da tafi kowace jiha a Nijeriya fama da ‘yan ta’addar Boko Haram.
Shima kansa Rarara dan Jihar Katsina ne kuma jiharsa na daga cikin jahohin Nijeriya masu fama da matsalar tsaro a yanzu, babu ta yadda za a ce bai damu da matsalar tsaro ba.
Saboda haka wannan zagin da kuke yi masa babu abin da zai hana shi kuma ba zai sa yayi abinda bai ga damar yi ba.
DUBA NAN: Zamu Iya Amfani Da Ramadana Wajen Magance Matsalolin Mu
Maganar karbar kwangila kuma masu karbar kwangila suna da yawa a Kannywood,da yawansu wasu ba don Allah suke nuna damuwarsu ba kwangila aka basu.