Wata budurwa ciki da kwarin guiwa ta je soshiyal midiya inda ta nuna damuwarta kan rashin abokin rayuwa.
Kamar yadda budurwar mai shekaru 40 a duniya tace, bata da ‘da ko daya na kanta kuma bata ko saurayi a yanzu.
Budurwar ta ja hankalin jama’a kan yadda ta dinga jimami tare da yi wa kanta jaje, lamarin da yasa jama’a suka dinga karfafa mata guiwa.
Wata budurwa mai shekaru 40 a duniya ta jajantawa kanta tare da bayyana cewa bata cikin farin ciki da yanayin da rayuwa ke tafiyar da ita.
A yayin wallafa bidiyonta a TikTok wanda ta bayyana cike da damuwa, budurwar ta rubuta cewa gata nan bata da ‘da balle miji.
Shekaruna 40, Babu Mashinshini Balle In Haihu, Budurwa Ta Koka a Bidiyo.
Budurwar mai takaicin yadda rayuwa ke tafiyar da ita ta kara da cewa bata da ko saurayi a halin yanzu kuma tayi kira ga Ubangiji da ya kawo mata dauki.
“Shekaru 40 yanzu, babu ‘da, babu miji kuma babu wata alaka. Oh ni Allah ka kawo min taimako.”
Ta rubuta a kasan bidiyon da tayi me taba zuciya.
Soshiyal midiya tayi martani
Tuni jama’a suka dinga jajanta mata tare da karfafa mata guiwa.
Ga wasu daga cikin martanin: Lina Lina66158 tace: “Kada ki cire rai Mama, ina da kawa mai shekaru 48 kuma ta ga ikon Allah, Yanzu haka tayi aure har da yara biyu.”
agmadalo2 tace: “Kada ki cire rai tawa, duk daya muke da ke. Lokacin da Ubangiji ya zaba mana shi ne daidai.”
Lawon9676yolo yace: “Allah zai share miki hawayenki kuma ya baki zabin zuciyarki.”
Secure the bag yace: “Muna fatan Allah ya baki abinda ki ke so, Ki dai cigaba da imani da Ubangiji.”
Jerrybenzo yace: “Ina da kawu mai shekaru 47 dake bukatar mace mai shekarun ki, ban sani ba ko kina da ra’ayi. A Legas yake zama.”
Jaydeeomani yace: “Kada ki cire rai ‘yan mata, shekaru 40 kacal ki ke. Za ki haifa yara.
Lokacin da Ubangiji ya zaba shi ne daidai.” Hotuna: ‘Dan Afrika ya kafa tarihin zama mutumin da yafi kowa hangamemen baki a duniya.
A wani labari na daban, wani ‘dan Afrika ya kafa babban tarihi a duniya bayan ya tabbata mutumin da yafi kowa katon baki a duniya, African Report Files ta ruwaito.
Kamar yadda aka gano, mutumin ‘dan asalin kasar Angola kuma hangamemen bakinsa yana daukan gwangwanin kacokan guda daya a bakinsa.
Source:legithausang