Batun bayyana wasu halittu da ake dangantawa da aljanun aliens a Jihar Katsina yana cikin abubuwan da suka dauki hankali a cikin wannan makon da ya gabata.
Kafafen sada zumunta na soshiyal midiya sun dauki zafi so sai ya yi bayyana wannan labari da masana suka ce babu wani abu mai kama da haka da ya shigo cikin kwaryar Katsina, abu ne kawai na wasu marasa kishin da hangen nesa.
Bidiyon halittar da ake yi wa lakabi da aljannun Aliens sun mamaye duk wasu shafukan sada zumunta tare da bayanin cewa wadannan Aljanu sun bayyana ne a garin Katsina, sai dai kuma babu wanda zai gaya maka ya gamsu ko kuma ya ga wanda ya gansu.
Jama’a da dama a jihar Katsina sun sha amsa kira daga wasu jihohi da kasashe dangane da wannan lamari, sai dai mafi yawan amsar da ake baiwa masu neman karin bayani ita ce, muma a soshiyal midiya muka gani kamar yadda kuka gani.
Kamar yadda Muhammad Aminu Kabir ya bayyana cewa abinda ya da ce mutane su tuna shine a irin wannan lokacin Manzon Allah (S) ya gaya mana cewa a lokacin Azumi ana daure Aljannu, wannan kadai ya isa jama’a su gane cewa wannan abun ba gaskiya bane.
Ya kara da cewa abu na biyu kuma ga duk wanda ya kalli bidiyon zai iya ganin hannun wani Bature wanda shi ya dauki bidiyon yayin da shi kuma wanda yake magana da Hausa faifan murya ne aka dora wanda ya yi dai dai da abinda ke faruwa cikin bidiyon.
“Hatta ma wata hallita ta Aliens da ake magana akanta tsawon lokaci a zahirance ma babu ita shirin fim ne na turawa, dan haka mutane suma daina sauraren wannan batun ko yada wadannan.
Ganin yadda wannan al’amari ke daukar wani sabon salo na tsoratar da jama’a musamman Katsina da ke fama da matsalolin tsaro yasa rundunar ‘Yan sanda ta jihar Katsina yin magana dangane da wannan tirka -tirka
Ba tare da bata lokaci ba kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina CSP Gambo Isah ya karyata wannan batu da ke yawo a kafafen sada zumunta na soshiyal midiya.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata samarwa da rundunar ta raba wa manema labarai a Katsina inda ta ce babu kamshi gaskiya a wannan lamari.
Sanarwar ta ce an jawo hankalin rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Katsina ne a kan wannan faifan bidiyo da ake yadawa cewa wasu aljanu sun shigo garin Katsina.
Sanarwar ta ce duk abinda aka gani acikin wannan faifan bidiyo karya ce tsagwaranta da wasu marasa kishi suka kirkira domin tayar da hankali jama’a a irin wannan lokaci.
Kamar yadda rundunar ‘Yan sanda ta ce wannan wani yunkuri ne na neman tada zaune tsaye da kuma kawo cikas a dorewar zaman lafiya da ake da shi a jihar Katsina
Kakakin rundunar ‘Yan sanda CSP Gambo Isah ya ce al’umma su yi watsi da wannan faifan bidiyo kuma tuni sun baza komar su domin damke duk wanda aka kama yana da hannu wajan kitsa wannan al’amari.