An cimma matsaya a karar da jarumi Ali Nuhu ya shigar gaban kotu kan Hannatu Bashir.
Sarkin Kannywood ya janye karar da ya shigar a kan jaruma kuma furodusa a masana’antar na shirya fina-finan Hausa.
Mai Shari’a Aminu Gabari ya umurci bangarorin jaruman biyu da su ci gaba da zaman lafiya a tsakanin su.
Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu, ya janye karar da ya shigar kan jaruma kuma furodusa Hannatu Bashir a gaban kotu, jaridar Aminiya ta rahoto.
Tun farko dai Ali Nuhu ya shigar da karar Hannutu ne kan zarginta da yake yi da ci masa mutunci ta hanyar aike masa sakonni.
Sai dai jarumar ta musanta zargin da yake mata na cin zarafinsa inda ta bayyana cewa maganganun da shi ya aike mata sun fi nata zafi amma ta dauke kai.
Jaruma Hannatu ta ce:
“Abin da ya fi bata min rai a wannan lamarin shi me da kansa Ali Nuhu ya zabi ranar da za a dauki fim din wato ranar 10 ga watan Oktoba sai dai bai halarci wurin daukar fim din ba kamar yadda ya yi alkawari haka kuma bai bayar da uzurin yin hakan ba.
“Hakan ya sa na rubuta masa sakon ta wayarsa inda kuma ya aiko min da maganganun da suka fi nawa zafi.
Sai dai ban ba shi amsa ba duba da cewa shi babba ne ya sa na bar maganar.”
An tattaro cewa jarumar bata samu damar halartan zama da aka yi na baya ba hakan ne yasa kotu ta tilasta mata zuwa da kai ba wai aiko yan sako ba.
Don haka, Hannatu ta yi zuwan kanta a zaman da aka yi na ranar Alhamis.
Sai dai kuma, lauyar Ali ta sanar da kotu cewa wanda take wakilta ya janye karar da ya shigar bayan sun yi sulhu a tsakaninsu da wacce yake kara.
Hakazalika, itama jarumar wacce ta halarci kotun da lauyoyinta uku ta yarda da batun janye karar.
Da fari dai alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari, ya nemi jin dalilin jarumar na kin halartar zaman kotun na baya, sai ta sanar cewa bata da lafiya ne a lokacin, hakan ya sa kotun ta yi mata afuwa.
A karshe kotun ta yi kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da zaman lafiya da juna.
Rikicin Ganduje da Rarara: Alan Waka Yace Kare Mutuncin Dauda Ya Fi Kamfen Din Takarar sa.
A wani labarin kuma, mun ji cewa alaka na kara tsami tsakanin shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara da gwamnatin jihar Kano karkashin Abdullahi Umar Ganduje.
Sai dai a wannan karon, shahararren mawaki kuma mai neman takarar kujerar dan majalisa a Kano karkashin jam’iyyar ADP, Aminu Alan Waka ya saka baki a rikicin.
Source:legithausang