Fitacciyar jaruma a Kannywood, Aisha Humaira, ta yi alkawarin biya wa marigayi darakta Aminu S. Bono duk bashin da ake bin sa.
“Idan so samu ne, kafin a yi jana’izarsa na sauke masa duk wani nauyi da ke kansa matukar bai fi karfina ba,” in ji ta.
A ranar Litinin Bono, wanda jarumi ne kuma darakta a masansa’antar ya rasu.
Rahotanni sun ce Bono ya dawo daga aiki ya ce ba ya jin dadi, jim kadan bayan hakan kuma rai ya yi halinsa.
“Sakamakon haka, ina kira ga duk wanda ya san cewa ya yi wata mu’amullar kudi da shi ko bashi, ko kuma ya karbi wani abinsa bai biya ba, in sha Allahu Rabbi, in dai har bai fi karfina ba, na yi alkawari in sha Allahu Rabbi zan sauke masa wannan nauyi,” in ji Humaira.
Bisa tsari na shari’ar Musulunci, ana so a biya wa duk wani mamaci bashin da ake bin sa kafin a birne shi.
Ta kara da cewa idan kuma har ya fi karfinta, za ta bi hanyar da za a sama masa taimako don a biya bashin.
Jarumar ta bayyana hakan ne a wani bidiyo mai tsawon minti uku da dakika 53 wanda ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Litinin tana zubar da hawaye.
Da yammacin ranar Litinin ne dai labarin rasuwar darakta Aminu S. Bono ya bulla, lamarin da ya sanya daruruwan ‘yan Kannywood girgiza.
Aisha ta kara da cewa idan kuma har ya fi karfinta, za ta bi hanyar da za a sama masa taimako don a biya bashin.
Jarumar ta bayyana hakan ne a wani bidiyo mai tsawon minti uku da dakika 53 wanda ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Litinin tana zubar da hawaye.
Da yammacin ranar Litinin ne dai labarin rasuwar darakta Aminu S. Bono ya bulla, lamarin da ya sanya daruruwan ‘yan Kannywood girgiza.
Source: LEADERSHIPHAUSA