Jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Zuwaira Saleh Pantami wadda aka fi sani da Adama a cikin shiri mai dogon zango na Dadin Kowa, ta bayyana yadda aka yanke mata hukuncin kisa a Saudiyya.
Ta bayyana haka ne, yayin wata hira da jaruma Hadiza Gabon a cikin shirinta na Gabon’s Room Show.
Ta bayyana yadda ta taka sawun barawo a kasar Saudiyya, har aka yanke mata hukuncin kisa.
Adama, ta bayyana cewa an taba yanke mata hukuncin kisa a kasar Saudiyya.
A cikin bayanin da ta yi tace sawun barawo ta taka Allah ne ya kubutar da ita, saboda ba ta aikata laifin da ake tuhumarta ba.
“Wani lokaci na je Umara, amma sai na tafi da irin tarkacen kayyayakin da ake tafiya da su daga nan Nalijeriya don na sayar a can,” in ji Zuwaira.
Ta ce na tafi da irin su daddawa, kuka, kubewa, goro da sauransu, “bayan na sayar sai na ga ribar da na samu har ta ninka jarin.
Sai kawai da na dawo Nijeriya sai na rika sarin irin wadannan kaya, ina tafiya da su Saudiyya, ina sayarwa, ina dawowa ina sake saye na koma.
“Na shafe lokaci mai tsawo ina yin haka, har sai ranar da aka kama ni wanda daga nan ne ban sake yi ba,” in ji ta.
Ta ce zuwan da ta yi na karshe wata rana tana cikin birnin Riyad, sai ta yi kacibus da wata kawa ta ‘yar asalin Sudan, sai ta nemi na rakata gida bayan na raka ta muna zaune a daki sai ga jami’an tsaro birjik.
Adama ta ce a nan aka tarkata dukkan matan da ke cikin dakin sai ofishin ‘yan sanda ,to a nan ne kawar tawa ta ce min gaskiya ke ba ki yi laifi ba, kin dai taka sawun barawo ne kawai.
Wannan kalami da jami’an tsaro su ka ji an yi a kai na ya yi sanadiyyar kubutata in ji Adama.
“Daga baya na gane ashe wai ana zargin sauran wadanda aka kama mu fa laifin kisan wani dattijo.”
Adama ta ce a karshe dai ita an sallame ta, amma sauran su bakwai duk an yanke masu hukuncin kisa.
Source LEADERSHIPHAUSA